Muhawara Hausa
 

 
EsinIslam Media: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Bincike Akan Wannan Batun:   
[ Jeka Gidan Dandalin Watsa Labarai | Zaɓi Sabon Taken ]

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (1)
(Labarin Cikakkun... | 7634 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (1)

Huduba ta Farko:

Hamdala da Taslimi da Mukaddima:

Bayan haka! Ya ku bayin Allah! A 'yan kwanakin nan Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi (Hafizahullah) ya yi rubutu da tsokaci game da siyasar Najeriya, inda ya ba da shawarwari da nasihohin da za su kawo wa kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya yi kira tare da jan hankali ga manyan jam'iyyun siyasar kasar nan wato PDP da APC da wasu daga cikin 'yan takararsu, Janar Buhari da Shugaba Jonathan cewa, domin maslahar Najeriya, ya kamata Janar Buhari da Shugaba Jonathan su hakura da takara. Domin takararsu na iya jefa Najeriya cikin hadari na tashin hankali da rudani. Ya kawo dalilansa na yin tsokacin da har ya kai ga rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Janar Buhari da Shugaba Jonathan. To, amma fitar wannan bayani ke da wuya, sai wasu magoya bayan Janar Buhari da wasu mabiya son zuciya suka yi ca a kan Malam, mai zagi na yi, mai zambo na yi, mai habaici na yi. Har da masu tsinuwa da la'ana duk na gani kuma na karanta kuma na saurare su. Ba ma wannan kadai ba, wasu marasa kunya har cewa suka yi wai Sheikh Ahmad Gumi sai da ya sha ya bugu sannan ya rubuta wannan wasika zuwa ga Janar Buhari. Wasu kuma har tsagerancinsu da rashin tarbiyyar ya kai su ga cewa wai, Dokta Ahmad ba dan Sheikh Abubakar Gumi ba ne na halak. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Wannan wane irin zance ne na jahilci? Wannan wace irin al'umma ce muke rayuwa a cikinta da ba ta san inda ke yi mata ciwo ba?

Ya ku bayin Allah! In takaice muku labari, wallahi a cikinsu har da masu cewa wai Atiku ne ko Kwankwaso ko PDP ko Yahudawa ne suka saye Malam ya yi musu aiki. Da masu cewa wai, kuskure ne malamai su tsoma baki cikin siyasa, kamata ya yi su zuba ido su yi kallo su kame bakinsu game da siyasar kasar nan. Maganganu iri-iri na shirme da wawanci wallahi da ka saurare su, ka san mai yin su kodai jahili ne, ko mabiyin son zuciya.


(Labarin Cikakkun... | 7634 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Matsayin sada zumunta a Musulunci
(Labarin Cikakkun... | 6854 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Matsayin sada zumunta a Musulunci

Ma'anar sada zumunci:

Sada zumunta shi ne kyautatawa da jinkai da bibiyar 'yan uwa (ma'abuta zumunta), ta hanyar sadar da dukkan alheri gare su da kawar da dukkan sharri daga gare su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu'ar alheri, duk bangare ne na sada zumunta.

Har ila yau, ma'anar zumunta na game yin sallama ga dan uwa yayin haduwa da gaishe shi da ce masa yarhamukallahu idan ya yi atishawa ya ce alhamdulillahi.

Sannan zuwa duba dan uwa yayin da yake rashin lafiya da jajanta masa kan wata asara da ya yi da taya shi farin cikin samun wani alheri da rufa masa asiri da rike amanarsa da kare mutunci da martabarsa a kan idonsa ko a bayansa a boye ko a bayyane da yi masa nasiha da shawara ta alheri duk sada zumunta ne.


(Labarin Cikakkun... | 6854 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
(Labarin Cikakkun... | 6897 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu

Hoton Bakan-Gizo

Allah cikin ikonSa Ya yi halittu iri daban-daban, wasu ana ganinsu wasu kuma, sun fi karfin mutum ya gansu. Daga cikin wadanda ba a iya gani da ido akwai iskokai/aljanu da mala'iku da abubuwan da dan Adam ke amfani da su irin iskar da ake shaka da yunwar da ke damunsa da sauransu. Malam Maharazu Barmu Kwasare ya taskace tarihin wani bakan-gizo da ya yi sanadiyyar mutuwar wadansu mutum shida da suka tarar da shi a cikin rijiya ba tare da sun san yana ciki ba. Al'amarin ya faru a 1396 Bayan Hijira wadda ta yi daidai da 1975 Miladiyya, kuma lokacin Malam Maharazu na da shekara 59 a duniya. Ya sanya wa wakar suna "Wakar Jinni Sago". Malam Maharazu ya kira sagon da jinni domin ba a ganinsa. Halittar da ba a gani kuwa, ga Bahaushe ko dai mala'ika ko kuma aljani. Idan aka samu wadanda ba su ba kuma ba a ganinsu, to mai yuwuwa ne suna tare da aljanu.

Sago na da sunaye daban-daban da ake kiransa da su. Wannan bambancin sunayen ya jibinci wurare da al'ummar da ke zaune a can. Wadansu mutane na kiransa sago wadansu kuma, bakan-gizo suke kiransa. Akwai masu kiransa zunni wadansu kuma, masha-ruwa suka fi saninsa da shi.

A wancan shekara ce jama'ar Unguwar Rungumi da ke cikin garin Sakkwato suka himmatu domin gyara wata tsohuwar rijiya don magance karancin ruwan sha. Duk kokarin da suke yi na hada aikin gayya a gyara rijiyar babu wanda ya san akwai bakan-gizon a cikinta. Da sun sani da ba su shiga ciki ba amma da yake Allah Ya kaddaro musu wannan lamari, babu mahani ga faruwarsa. Domin tabbatar da wurin da abin ya faru, ga abin da Malam Maharazu ya ce:


(Labarin Cikakkun... | 6897 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
(Labarin Cikakkun... | 7944 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da sunan addini – Suleiman Danyaro

By Bashir Yahuza Malumfashi

Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai

Ana ta kai-komo da bayanai game da tsarin almajirci a Najeriya. Malam Suleiman Danyaro ya wallafa littafinsa mai sunan: ‘Almajirai Ko Attajirai?' wanda kirkirarren labari ne, inda a ciki yake ba da labarin wani almajiri wanda tsarin da ya bi ya yi Karatun Allo ya sha bamban da irin wanda yara suke yi a Arewacin Najeriya. A tattaunawarsa da Aminiya, marubucin ya bayyana cewa ya rubuta wannan littafi ne domin ya fadakar da al'umma cewa ba lallai ne sai an tura yara bara ba ake samun ilimi.

Mene ne takaitaccen a tarihinka?

To da farko sunana Suleiman Danyaro. An haife ni a ranar 6-8-1966 a Tudun Wada Kaduna. Tun ina karami aka sa ni a makarantar allo. Sai a 1973 aka sanya ni a makarantar firamare, wacce ke harabar Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna, (Kaduna Polytechnic), a nan Kaduna. Na gama makarantar sakandare ta jeka-ka-dawo da ke Tudun Wada Kaduna, wacce ake kira da Maimuna Gwarzo a 1985.

A bangaren aiki ko sana'a kuwa, na taba dinki da kasuwanci na tsawon shekara bakwai. Bayan haka na koma karatu a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna, inda na samu shaidar Babbar Diploma (HND) a fannin Al'amuran Kasuwanci. Yanzu haka ina wakiltar kamfanoni biyu na man fetur masu zaman kansu, wato Ango Joint Petroleum da kuma Alkaram Petroleum a Matatar Mai ta Kaduna. Kuna ni ne Sakataren Kudi na Arewa na Kungiyar Kananan Ma'aikatan Man Fetur Masu Zaman Kansu (IMB/NUPENG).


(Labarin Cikakkun... | 7944 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
(Labarin Cikakkun... | 10252 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana

By Sadik Tukur Gwarzo

Wata bishiyar kuka

Kasancewar akwai ilimi a cikin kowanne abu, ya kamata mu yi dubi ga bishiyoyin kuka don fahimtar ilimin da suke sanar mana a nan kasar Hausa Domin kuwa kamar yadda masana kimiyyar duwatsu ke cewa akwai tarihi a kowane dutse, haka ma akwai labari ga mafi yawan rukunonin bishiyoyin kuka a nan kasar Hausa. To amma, wane labari bishiyoyin suke sanar mana?

Ana gane wanzuwar biranen Hausawa daga kukoki

Hakika, kasancewar tunda jimawa, babu shahararrun gine-gine masu kafuwa cikin kasa a kasar Hausa, muna iya cewa babu wani ma'auni da ke tabbatar mana da wanzuwar tsohuwar rayuwa a kasar Hausa sama da rukunin kukoki.

Ko tantama babu, duk inda aka samu kukoki sun jeru reras, ko sun yi da'ira, ko wani abu mai kama da haka, to akwai labarin cewa gari ya taɓa wanzuwa a wannan wuri.Ana sanin tsufan gari gami da tumbatsarsa daga kukoki.


(Labarin Cikakkun... | 10252 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
(Labarin Cikakkun... | 7337 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakkwato

By Nata'ala Sambo Babi (Nasaba)

Nasabarsa

Sunansa Usman dan Malam Is'haka dan Malam Umar, ana yi masa alkunya da (Dan Is'haka). Dan kabilar Toradde ne, wata kabila da ta fito daga Futa Toro ta kasar Mali suka zo suka zauna a kasar Hausa, wadanda ake kiran shugabansu da Malam Musa Jakwallo.

Haihuwarsa

An haife Usman bin I'shaka (Dan I'shaka) a cikin garin Sakkwato, shekara biyu da rasuwar Shehu Usman Dan Fodiyo wato, a shekara ta 1234 Bayan Hijira, wadda ta yi daidai da 1819 Miladiyya.

Malamai sun ce, kafin hakan Malam Is'haka ya yi mafarkin ya ga rijiya cike da ruwa a cikin gidansa, mutane sun kewayeta suna sha daga ruwanta. Sai Malam Is'haka ya ji tsoro kwarai da gaske da wannan mafarki. Da safiya ta yi sai ya je ya gaya wa sheikh Usman bin Fodiyo wannan mafarki, sai mujaddadi ya ce, da shi kada ka ji tsoro a kan wannan mafarki, nan gaba INSHA ALLAHU, Allah zai arzuta ka da haihuwar wani yaro mai albarka mai ilimi, wanda zai kasance madaukaki, kuma sunansa zai watsu ko'ina a cikin garuruwa saboda yawan iliminsa. Idan Allah Ya arzuta ka da wannan da, to, ina rokonka da ka sanya masa sunana.

Bayan mafarkin sai matar Malam I'shaka ta samu juna biyu bayan ta haihu sai ta haifi yaro, sai mahaifinsa ya sanya masa suna Usman domin neman samun albarka da kwadayin ya zama malami mai halayen kirki.


(Labarin Cikakkun... | 7337 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Adabin Gargajiya
(Labarin Cikakkun... | 4157 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Adabin Gargajiya

By Faruk Tahir Maigari

Tun asali a ƙasar Hausa, akwai hanyoyi da Hausawa ke bi wajen gudanar da rayuwarsu da kuma isar da saƙonni ta kowace fuska kama daga karantarwa da zaburarwa, da nishaɗantarwa da gargaɗi da sauransu. Dukkan waɗannan abubuwa akan yi su ne a gargajiyance da baki. Misali, a kan bi hanyar waƙa wajen zaburar da mutum kamar mafarauta, 'yan dambe da sauransu. Haka akan bi hanyar tatsuniya wajen koya wa yara kyawawan ɗabi'u ta hanyar labaran tatsuniyar.

Saboda haka wannan tsohuwar hanya, ta karantarwa da sauransu da baki ake yin ta, ba a rubuce ba. Don haka ne masana suka kira ta Adabin Gargajiya.

Aminiya ta yi waiwaye a kan adabin gargajiya domin kalato wadansu bayanai daga masana domin amfanar mai karatu da kuma daliban ilimi. A kan kira wannan rubutu dake tafe Adabin Gargajiya kuma a kan kira shi da Adabin Baka.

Aminiya ta yi wannan waiwaye ne domin dora masu karatu a kan yadda duk lokacin da za su yi karatu su fahimci fagen da suke karantawa.

Ma'anar Adabin Gargajiya


(Labarin Cikakkun... | 4157 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
(Labarin Cikakkun... | 4463 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa

By Aliyu Babankarfi Zariya

Farfesa Umaru Balarabe Ahmed

Masanin adabin Hausa da wasan kwaikwayo Farfesa Umaru Balarabe Ahmed, ya samu lambar yabo ta kasa.

Shugaban Hukumar Gudanarwar Majalisar Bada Lambar Yabo ta Kasa, Farfesa Shekarau Yakubu Aku ya ce ana zabo mutanen da ake ba su lambar yabo ne saboda gudunmawar da suka ba da ga ci gaban kasa.

Ya bayyana haka ne a lokacin taron laccar ba da lambar yabo karo na biyu na bana da aka gudanar a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Farfesa Shekarau Yakubu Aku ya ce duk mutanen da aka bai wa lambar yabo ta kasa, mutane ne da suka ba da gudunmawa wajen ci gaban kasa kuma wadanda suka yi fice a duniya a fannoni daban-daban na rayuwar dan Adam da suka hada da ilimi da al'adu da kimiyya da fasaha da kere-kere.

Ya ce ana gudanar da taron laccar ba da lambar yabon ne domin bayyana batutuwan da mutanen da aka bai wa lambar yabon suka yi na ci gaban kasa domin janyo hankalin 'yan Najeriya.


(Labarin Cikakkun... | 4463 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Matsara Wasu Yan Bidi'ah Da Wasu Kafurai Ta Yi Matukar Kama Game Da Khawaar
(Labarin Cikakkun... | 4730 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Ibrahim Jalo Jalingo

Matsara Wasu Yan Bidi'ah Da Wasu Kafurai Ta Yi Matukar Kama Game Da Khawaarijan Boko-Haram

Matsayar wasu daga cikin 'yan bidi'ar kasan nan, da wasu daga cikin kafuran kasan nan ta yi matukar kama game da abin da ya shafi Khawarijawan Bokoharam.

Dalili kuwa shi ne:-
1. Wasu daga cikin kafuran wannan Kasa tamu suna nan suna ta cewa: Dukkan wani musulmi dan bokoharam ne! Dalilinsu na nazari a kan wannan ikirari shi ne: 'Yan bokoharam da sauran musulmai Annabinsu daya ne, Alkur'aninsu daya ne, matsayarsu game da rukunai biyar din nan na Musulunci daya ne, matsayarsu game da dukkan wani mutumin da bai yi imani da Alkur'ani da Annabi ba daya ne! A dai nazarce su kan iya lissafa abubuwa da yawa bayan wadannan da aka ji yanzu kuma su ce 'Yan bokoharam da sauran Musulmin Kasar nan ba su da wani sabani ko banbanci a cikinsu!!

Wasu daga cikin 'yan bidi'ar wannan Kasa tamu suna nan suna ta cewa: Dukkan wani Ahlus Sunnah a wannan Kasa tamu dan bokoharam ne! Dalilinsu na nazari a kan wannan likirari nasu shi ne: 'Yan bokoharam da sauran Ahlus Sunnah sun yarda da Kitaabut Tauheed na Sheikh Muhammad Bin Abdil Wahhab, kuma dukkansu sun yarda da littattafan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah, kuma dukkansu suna kiran kansu Ahlus Sunnah Wal Jama'ah! A dai nazarcen su kan iya lissafa wasu abubwa da yawa bayan wadannan da kuka ji, sannan su ce 'yan bokoharam da sauran Ahlus Sunnan Kasar nan ba su da wani sabani a cikinsu!!


(Labarin Cikakkun... | 4730 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Nigeria Ba Ta Bukatar Maha'inta Maciya Rashawa
(Labarin Cikakkun... | 3363 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Dr. Jamilu Zarewa, Fatawoyi

Nigeria Ba Ta Bukatar Maha'inta Maciya Rashawa

Har yau har gobe nigeria tana bukatar jagorancin mutanen da sam ba a san su da cin hanci da rashawa ba; mutanen da suka yi kuruciyarsu, da manyantakarsu cikin hidimar kasa da 'yan kasa ba tare da mahankalta sun tuhume su da ha'intar al'ummar da suke jagoranta ba domin arzutta kawunansu.

Har kullum idan talakawa suka sami damar yin zabi tsakanin: 'yan siyasar da suka yi kuruciyarsu da manyantakarsu cikin hidimar kasa da 'yan kasa ba tare da ha'intar al'ummah ba, da kuma 'yan siyasar da mahankalta ke tuhumar su da ha'intar al'ummah, to lalle wajbi ne a kan su talakawan su tashi tsaye su zabi kaso na farkon, su yi watsi da kaso na biyun komin kaifin bakinsa da iya yin sharri da yarfensa.

Sam babu alheri cikin dukkan wani kawance, ko hadaka da yake yin kokarin kawar da masu kokarin yin yaki da rashawa da ha'intar al'ummah domin dasa kishiyoyinsu.


(Labarin Cikakkun... | 3363 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Ba Daidai Ba Ne A Daidaita Kashe Sheikh Ja'afar Da Kashe Wasu 'Yan Tar
(Labarin Cikakkun... | 2361 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Ba Daidai Ba Ne A Daidaita Kashe Sheikh Ja'afar Da Kashe Wasu 'Yan Tarzoma

Tabbas nau'i ne na zalunci wani ya yi mukaranar kashe malamai masu kiran mutane zuwa ga yin riko da sunnar Annabi mai tsira da amincin allah; kamar sheikh ja'afar mahmud adam, da makamancinsa, da kashe wasu 'yan tarzoma daga cikin 'yan bidi'ah a lokacin da suke yi wa daula tarzoma da khuruuji da halattattun jami'an tsaro suka yi domin kare doka da oda da kuma haibar daulah. Lalle irin wannan mukarana tsagwaron zalunci ne da jahilci tare da son zuciya suke haifar da shi.

Abin da masu ilmin musulunci da tarihi za su fada a nan shi ne kamar haka: wasu khawaarijawa sun tsara yadda za su kashe wani babban sahabi mai yawan daraja, mai kuma yin kira zuwa ga sunnar annabi mai tsira da amincin allah; watau khalifah aliyyu bin abi taalib allah ya kara masa yarda, kuma sun je sun sami nasarar kashe shi din shi kadansa a lokacin da yake yin sallar asubahi ko yake yin haramar sallar asubahi tare da sauran musulmi da yake yi wa limanci a babban masallacin garin kufah.


(Labarin Cikakkun... | 2361 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Wai Da Gaske Ne Ja'far Mahmud Adam Da Albaniy Zaria Ba 'Yan Salafiyyah
(Labarin Cikakkun... | 4375 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Dr Kabir asgar wrote

Wai Da Gaske Ne Ja'far Mahmud Adam Da Albaniy Zaria Ba 'Yan Salafiyyah Ba Ne?

1- Mutane da yawa suna ta tambaya ta ta hanyoyin sadarwa dabam-dabam akan maganganun da wasu suke ta yi na kokarin fitar da Mal. Ja'afar Mahmud Adam da Mal. Auwal Albaniy Zaria (Allah ya gafarta musu) daga tawagar salafiyyah.

2- A kashin gaskiya ni ba na ganin dacewar yin ce-ce-ku-ce akan ire-iren maganganu na mutane masu bin irin wannan tafarkin. Saboda ni ba malami ba ne, ballantana a ce mujtahidi wanda zai iya yin hukunci na jarhi da ta'adili akan mazaje. Sannan kuma ina da abubuwa masu tarin yawa da na sa a gaba nake yi wadanda nake ganin sun fi mini muhimmanci fiye da shiga sharo-ba-shanu. Bugu da kari, a dabiata ina matukar kyamar jayayya da kokarin kare wani mutum ko aibata shi don kashin kansa ko don cim ma wata manufa wacce ba ta da alaqa da asalin addini ko kuma jayayya da mutumin da ya riga ya gamsu da abin da ya fahimta. Don haka, zan yi wannan tsokacin ne bisa tilas, ba dan ina so ba sai da bayyana abin da na fahimta ga wadanda ke da budaddiyar zuciya da ke iya sauraron bangarorin sabani ba tare da jafa'i ko son zuciya ba.

3- Gaskiya ne aqidar Ahlus Sunnah ta tsayu akan lazimtar da jama'a da hani akan fito-na-fito da masu mulki. Kuma gaskiya ne akwai wasu maganganu da Mal. Ja'afar ko Mal. Albaniy Zaria suka yi wadanda a zahiri za ka ji su da zafi ko kausasawa ko fushi, musamman in ka dubi maganganun a tsurar su ba tare da la'akari da abin da ya haifar da su ba. Irin wannan zantukan na iya zamowa abin kafa hujja ga wanda bai san su ba ko kuma wanda dama can yana da wata manufa, ko kuma wanda ya riga ya yanke hukunci sannan ya tafi neman dalilin da zai goyi bayan hukuncinsa.


(Labarin Cikakkun... | 4375 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

YIWA IYALAN MAMACI GAISUWA (TA-AZIYYA)
(Labarin Cikakkun... | 3118 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

YIWA IYALAN MAMACI GAISUWA (TA-AZIYYA)

Ya halatta ayiwa iyalan wanda akaiwa rasuwa gaisuwa amma akula da abubuwa kamar haka:-

1-Yin gaisuwa da abinda zai sanyaya musu rai ya rage musu zafin rabuwa ya sanyasu cikin yadda da kaddara da hakuri da duk abinda ya kamata in bai sabawa sharia ba.

2-Yin addua kamar haka:(INNA LILLAHI MA AKHAZA WA LILLAHI MA A ADA WA KULLU SHAI IN INDAHU ILA AJALIN MUSAMMA FALTASBIR ALTAHTASIB).

3-Ta aziyya bata wuce kwan uku duk lokacin da aka hadu sai ayita.

4-Akauracewa abubuwa biyu:
1-Taruwa awaje keban tacce kamar gida ko masallaci ko maqabarta.
2-Yin abici da yan uwan mamacim sukeyi dan walima ga wanda suka zo ta aziyya.

5-Sunnah shine yan uwa da makota su hadawa iyalan mamacin abinci.


(Labarin Cikakkun... | 3118 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

4. NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA, UWA CE GARE NI FITOWA TA 3
(Labarin Cikakkun... | 1494 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

4. NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA, UWA CE GARE NI FITOWA TA 3

(Masoyinki ya rabauta, makiyin ki ya yi hasara)

ADDU'AR MANZON ALLAH, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI, GA NANA AISHA:

Daga Nana Aisha, Allah ya kara yarda a gare ta, ta ce: lokacin da na ga tsarkin zuciyar Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai na nemi ya roka mun Allah, sai ya ce:

''Yaa Allah ka gafarta wa Aisha abin da ya gabata na zunubanta, da wanda ya jinkirta, da wanda ya bayyana da wanda ya boyu'', sai ta yi dariya har sai da ta dora kanta a bisa cinyoyin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, saboda dariya.

Sai ya ce da ita: '' Addu'ata ce ta sanya ki farin ciki?!. Sai ta ce: me ya sanya addu'arka ba za ta sanya ni farin ciki ba?. Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ''ina rantsuwa da Allah, wannan ita ce addu'ata (gare ki).


(Labarin Cikakkun... | 1494 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

3. NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA, UWA CE GARE NI FITOWA TA 2
(Labarin Cikakkun... | 1676 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

3. NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA, UWA CE GARE NI FITOWA TA 2

(Masoyinki ya rabauta, mai makiyin ki ya yi hasara)

SOYAYYAR MANZON ALLAH, TSIRA DA AMINCIN ALLAH, TABBATA A GARE SHI, GARE TA:

Allah ta'ala shi ya zabawa ManzonSa, tsira da amincin Allah su tabbatar a gare shi, Nana Aisha ta kasance Matar Aure a gare shi kamar yanda ya zo a cikin ingantattun littafan hadisin Bukhari da Muslim, Allah ya yi rahama a gare su. Ga lafazin Imamu Muslim:

Daga Aisha, Allah ya kara yarda a gare ta, ta ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce:

''An nuna mun ke a cikin mafarki, har darare uku (3), Mala'ika yana zuwa mun dake lullube cikin mayafin alhariri, sai ya ce dani:


(Labarin Cikakkun... | 1676 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

2. NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA, UWA CE GARE NI & 1. WACE CE NA
(Labarin Cikakkun... | 2114 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

2. NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA, UWA CE GARE NI & 1. WACE CE NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA???

(Masoyinki ya rabauta, mai zagin ki ya yi hasara)

Dukkan yabo, godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su qara tabbata ga Manzon Rahama, tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi, Sahabbansa da Iyalansa Iyayen Muminai bisa nassin al-Qur'ani.

'Yan uwa, sananniyar Magana ce cewa inda za a taskace dukkan takardu da alqaluma ba za su iya rubuce daraja da matsayin uwar Muminai Nana Aisha, Allah ya qara yarda a gare ta ba, sai dai zuciyata, ta nutsu akan in rubuta 'yar taqaitacciyar saqo, wanda zai qara taimakawa qananan dalibai irina wajen qara fito mana da wasu daga cikin abubuwan da ya kamata mu sani game da ita.

1. WACE CE NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA???


(Labarin Cikakkun... | 2114 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

ZUNUBI CUTANE, TUBA KUMA MAGANINE
(Labarin Cikakkun... | 8176 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

ZUNUBI CUTANE, TUBA KUMA MAGANINE

Kowanne cuta da Allah Subhanahu Wata'ala Ya yita ya sanya abinda ya kasance shine maganin wannan cutar sai dai ba dolene dan Adam Ya kai ga wannan Maganin a lokacin da yake bukata kodai saboda karancin ilimin mu ko kuma rauninmu.

Mafi girman cuta dake halaka bawa itace zunubi (sabon Allah) domin bata gushe wajen jefa mutum kunci anan duniyaba hasalima mai wannan cutan zaifi cutuwa a bayan Mutuwarsa, Cikin Falalar Allah Da RahmanSa Wannan cuta ya san mata abinda ya zama magani har ma da rigakafin don kaucema kamuwa da ita.

Maganin wannan cuta kuwa shine TUBA DA NEMAN GAFARAR ALLAH a cikin dukkan zunubanmu wadanda muka sani da wadandama bamu san mun aikataba.

Allah Subhanahu Wata'ala Yace; ‎ﻭﺗﻮﺑﻮﺍ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪﺟﻤﻴﻌﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥﻟﻌﻠﻜﻢﺗﻔﻠﺤﻮﻥ Kutuba Zuwa ga Allah gaba daya yaku Muminai tabbas zaku rabauta. {suratul Nur 31} Allah Subhanahu Wata'ala Yace; ﺇﺳﺘﻐﻔﺮﻭﺍ ﺭﺑﻜﻢﺛﻢﺗﻮﺑﻮﺍ ﺇﻟﻴﻪ ku nemi gafarar ubangijinku sannan ku tuba gareshi. {Suratul hud 3} ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻳﻘﻮﻡ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﺣﺘﻰ ﺗﻨﻔﻄﺮ ﻗﺪﻣﺎﻩﻓﻘﻠﺖ ﻟﻪ: ﻟﻢ ﺗﺼﻨﻊ ﻫﺬﺍ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪﻭﻗﺪ ﻏﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻚ ﻣﺎ ﺗﻘﺪﻡ ﻣﻦ ﺫﻧﺒﻚ ﻭﻣﺎ ﺗﺄﺧﺮ!

ﻗﺎﻝ'' : ﺃﻓﻼ ﺃﺣﺐ ﺃﻥ ﺃﻛﻮﻥ ﻋﺒﺪﺍ ﺷﻜﻮﺭﺍ'' ( (ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ .


(Labarin Cikakkun... | 8176 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

MUTANE DA DABBOBI SUN YI KAMA ( 1 )
(Labarin Cikakkun... | 2892 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

Dr. Mansur Sokoto

Mutane Da Dabbobi Sun yi Kama ( 1 )
'Yan uwana Assalamu Alaikum.

Da yawa daga cikinmu sun taba karanta wannan ayar – koma in ce, sun sha karanta ta – inda Allah yake cewa:

"Babu wata dabba mai tafiya a doron kasa, ko wani tsuntsu da yake tashi da fukafukansa face suma al'ummomi ne masu kama da ku.

Ba mu rage kome daga wannan littafi ba.

Sannan zuwa ga Ubangijinku ake tattaraku" [Al- an'am:38].

Amma kadan ne daga cikin masu karanta wannan ayar suka tsaya cikin nutsuwa suka yi tunani game da sirrin da yake cikin wannan ayar. Ka dubi ayar sarai, ka kula da abin da Allah ya nuna a cikinta, na cewa dabbobin da suke tafiya a kan doron kasa da masu tashi a sararin sama'u, duk al'ummomi ne masu kama da mu, mu mutane. Ta ina ne dabobi da tsintsaye suka yi kama da mu?


(Labarin Cikakkun... | 2892 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI?
(Labarin Cikakkun... | 2612 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI ?

Manyan malamai sunyi kokarin tattara, manyan laifukkuka, a guri guda domin sanin su, da fahimtar munin su, da yadda zaa guje musu.

Allah ya bamu ikon kiyayewa.

1- Shirka da kashe-kashenta 2- kisan kai 3 – Tsafi 4- Wasa da sallah 5- Hana zakka 6- Sabawa iyaye 7- Cin riba 8- Cin dukiyar marayu 9- yiwa Annabi saw karya 10- Karya Azumi da gangan 11- Gudu daga filin daga ana yakin kare addini.

12- Yin Zina 13- Shugaba mai hainci ga talakawansa.

14- Shan giya da sarrafata 15- Girman kai da takama da jiji da kai 16- Shedar Zur 17- Luwadi da mdigo 18- Yin kage ga muminai 19- Satar dukiya daga baitul mali 20- Zaluncin cin dukiyar jamaa, ta algus da manuba.

21- Sata, da sane.


(Labarin Cikakkun... | 2612 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

MARABA DA WATAN RAMADAN
(Labarin Cikakkun... | 4971 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)

LAILATUL QADR

MARABA DA WATAN RAMADAN

LAILATUL QADR: shine Qaddararren dare, dare mai daraja mai girma, daren alkhayri, dare mai albarka, dare ne wanda misali bazai gama rarrabe abunda wannan dare ya qunsa ba face ALLAH (SWT) shine masani.

•••FALALAR DAREN LAILATUL QADR••• .

Falalar wannan dare mai girma ce domin an shedar da sauqar al'qur'ani acikinsa, kuma ALLAH (SWT) Ya ambace sa acikin LittafinSa a wurare daban-daban, daga cikinsu akwai fadar ALLAH (SWT):

"lallai mu muka sauqar da shi (Alqur'ani) acikin daren Lailatul Qadr, me ya sanar da kai abunda ake qira Lailatul Qadr, Daren Lailatul qadr yafi daraja akan wata dubu, saboda mala'iku suna sauqa acikinsa tare da ruhu (jibril) da izinin Ubangijinsu ga kowane al'amari, Amincin ALLAH ne wannan daren (da abinda ke cikinsa) har 6ullowar alfijir" .

(Surah ta 97 aya ta 1 zuwa 5)
Haqiqa daukakar daraja ta isa ga wannan dare na Lailatul Qadr acikin wadannan ayoyi cewa yafi watanni dubu, Haka kuma sauqar mala'iku acikinsa har da Mala'ika Jibrilu (AS) wata falala ce ta wannan daren.


(Labarin Cikakkun... | 4971 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 5)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

MUNAFUKAI BA SAHABBAI BANE GABATARWA
(Labarin Cikakkun... | 12765 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

MUNAFUKAI BA SAHABBAI BANE GABATARWA

ﺃﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻦ ﺑﻪ ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪًﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ، ﺃﻣﺎ ﺑﻌﺪ: ﻓﺈﻥ ﺃﺻﺪﻑ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ، ﻭﺃﺣﺴﻦ ﺍﻟﻬﺪﻱ ﻫﺪﻱ ﻣﺤﻤﺪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﻭﺷﺮ ﺍﻷﻣﻮﺭ ﻣﺤﺪﺛﺎﺗﻬﻤﺎ، ﻭﻛﻞ ﻣﺤﺪﺛﺔ ﺑﺪﻋﺔ، ﻭﻛﻞ ﺑﺪﻋﺔ ﺿﻼﻟﺔ، ﻭﻛﻞ ﺿﻼﻟﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ .

ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺻﻞ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤﺪ ﻛﻤﺎ ﺻﻠﻴﺖ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ﺇﻧﻚ ﺣﻤﻴﺪ ﻣﺠﻴﺪ، ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤﺪ ﻛﻤﺎ ﺑﺎﺭﻛﺖ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ﺇﻧﻚ ﺣﻤﻴﺪ ﻣﺠﻴﺪ .

Bayan haka; nazabi nayi rubutu ne akan wannan mas'alar domin shubuhar da ake kawowa al'ummar annabi.

Yawanci idan mu ahlussunnah mukayi rubutu gameda ayoyinda suke magana akan falalar sahabbban manzon Allah SAW gaba dayansu, sai kaji masu wata batacciyar aqida suna cewa ai ba dukkan sahabbai ake nufi ba.

tunda ai munafikai suna ciki, harma wasu suce maka yawancin sahabban duk munafikai ne.


(Labarin Cikakkun... | 12765 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

ALAMOMIN TASHIN AL- KIYAMAH GUDA 'DARI 100 KASHI NA BIYU (2)
(Labarin Cikakkun... | 3041 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

ALAMOMIN TASHIN AL- KIYAMAH GUDA 'DARI 100 KASHI NA BIYU (2)

MAL.AMINU IBRAHIM DAURAWA

51.

Wani Zamani da mutum zai kwana Mumini ya wuni kafiri;- saboda mafi yawan maganganu da aiyuka da ba sa kan Shari'ah 52. 'Kawata Masallatai da yin gasar Hakan (kaji ana Masallacin mu yafi naku kyau) 53. 'Kawata gidaje da yi musu kwalliya 54. Yawan Saukar Kwarankwatsa da Aradu 55. Yawan Rubuce-Rubuce;- Ya'duwar Rubutuce-Rubuce marasa amfani (jaridu da mujallu, da littafai da internet) ba a tunanin amfanin rubutun kawai da an rubuta 56. Wanda suka 'kware a ro'ko da ziga, su suka fi samun ku'di 57. Za shagala da karanta wasu abubuwa a bar Al'qur'ani 58. 'Karancin Malaman fi'khu da yawan Gardawa 59. Neman Ilimi a wajen 'kananan mutane;- 'karamin Mutum wanda ba ya aiki da ilimin sa 60. Yawan mutuwar ba-zata 61.

Shugabancin Wawaye (kuma suna ganin kan su wayaiyu) 62. Lokaci zai dinga sauri 63. Banzaye za su mamaye kafafan ya'da labarai;- Mutumin da ba kowa ba, kuma bai zan komai ba, zai dinga magana kan abubuwan da suka shafi Al'ummah 64.


(Labarin Cikakkun... | 3041 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

ALAMOMIN KYAKYKYAWAN K'ARSHE!
(Labarin Cikakkun... | 1983 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Sheikh Isa Ali Pantami

ALAMOMIN KYAKYKYAWAN K'ARSHE!

Allah ya sa mu cika da IMANI,..

Annabi (SAW) yana cewa: Idan Allah yana nufin BAWANSA da ALHERI, sai yayi aiki da shi. Sai aka tamabayi Annabi (SAW) ta yaya Allah zai yi aiki da shi?

Sai yace:Allah zai shiryar da shi zuwa ga ayyuka na kwarai gabannin rasuwarsa (Imam Ahmad, 11625; al- Tirmidhi, 2142; saheeh by Al-Albaani ya inganta shi Saheehah, 1334).

ALAMOMIN CIKAWA DA MUTUWAR SHAAHADA:

Akwai wasu alamomi duk wanda ya rasu ya samu dacewa da daya daga cikinsu akwai alamar ya samu mutuwa mai nagarta, kuma akwai alamun yayi mutuwar SHAHAADA.


(Labarin Cikakkun... | 1983 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

GAISHE DA MARA LAFIYA
(Labarin Cikakkun... | 1142 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Sheikh Isa Ali Pantami

GAISHE DA MARA LAFIYA

ZUWA GAISUWAR MARAR LAFIYA BABBAR IBADA NE! Allah ya mana karin LAFIYA da IMANI,.... Imam Bukhari, Shaykhul Islam da Ibn Uthaymeen (Rahimahumul Laah)
dukkansu sun tabbatar da cewa zuwa gai da majinyaci wajibi ne.

Amma Bn Uthaymeen (RH) yana ganin cewa yana halatta wani ya wakilci wani a gaisuwa ko kuma zuwan wasu yasa wajibcin ya sauka kan wasu "Fardhu Kifaayah." Annabi (SAW) yana cewa: ku ciyar da Mai Jin Yunwa, ku ziyarci MARAR LAFIYA, sannan ku yanta Fursunoninku (Bukhari).


(Labarin Cikakkun... | 1142 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
(Labarin Cikakkun... | 7780 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DAGA JARIDAR AMINIYA

Kyauta da kyauta – yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)

Category: Rayuwar musulmi Published on Friday, 18 December 2015 15:23 Written by AHMAD MUHAMMAD Hits: 113 Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.

Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi'un Musulmi. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, mun kwana bayan mun koro bayani a karkashin kanun, ''Allah Yana sane kuma ana musanyawa,'' har muka kai daidai inda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, ''Dukiyar da take taskance ita ce wadda aka bayar da ita saboda Allah.'' A'isha (Allah Ya yarda da ita), ta ba da labarin wata tunkiya da aka yanka, aka yi ta rabon namanta, har sai lokacin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya tambayi ko me ya rage a cikinta, sai aka ce masa, ''Karfata daya.'' Sai ya ce, ''An taskance komai na tunkiya, sai karfata daya kadai.'' Imamu Tirmiziy ne ya ruwaito shi kuma ya ce Hadisi ne mai kyau, ingantacce.


(Labarin Cikakkun... | 7780 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

KYAUTA DA KYAUTA- YI DON ALLAH BA TA RAGE DUKIYAR MUSULMI
(Labarin Cikakkun... | 7955 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

DAGA JARIDAR AMINIYA

KYAUTA DA KYAUTA- YI DON ALLAH BA TA RAGE DUKIYAR MUSULMI

Kyauta da kyauta- yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi Category: Rayuwar musulmi Published on Friday, 11 December 2015 15:05 Written by AHMAD MUHAMMAD Hits: 155 Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.

Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi'un Musulmi. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.


(Labarin Cikakkun... | 7955 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

WANNAN KISAN KARE DANGIN DA KIRISTOCI SUKE MANA SUN SHIRYA SHINE TUN TSAWON SHEK
(Labarin Cikakkun... | 1435 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Daga: Engr Abu-Ameena Bn Khamis

WANNAN KISAN KARE DANGIN DA KIRISTOCI SUKE MANA SUN SHIRYA SHINE TUN TSAWON SHEKARA SITTIN BAYA

Allahu Akbar! Wannan maganar ta fito ne daga bakin wani mash-hurin malamin addinin musulunci a lokacin da ya kawo ma Ash-Sheikh Albaniy Zaria Rahimahlluah Ziyara a cibiyar ilimi na Daruul hadeethis Salafiyyah dake zaria.

Prof Dauda Ojobi yace:-

'' A lokacin da yake cikin addinin kiristanci a shekarar 1954. 'Kungiyar kiristoci ta Nigeria ta gabatar da taruka a Jos kuma shine sakataran tarukan a lokacin.


(Labarin Cikakkun... | 1435 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

SAKON SARKIN SAUDIYYA GA SHUGABAN NIGERIA BUHARI: MUKURKUSHE 'YAN SHIA DA A
(Labarin Cikakkun... | 2219 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

SAKON SARKIN SAUDIYYA GA SHUGABAN NIGERIA BUHARI: MUKURKUSHE 'YAN SHIA DA AKAI A ZARIA, YAKI NE DA TA'ADDANCI

Jibwis Nigeria ta leka kasar saudiyya, Inda na ruwaito wannan labari, kamar yadda Kuka sani Wannan shine karo na farko da Sarki salman yayi jawabi tun bayan murkurkushe 'yan shi'a a kwanakinnan. A tattaunawarsa da shugaba Buhari ta hanyar wayar salula, sarki Salman ya ambaci cewa kashe daruruwan yan Shia a birnin zaria shima yaki ne da ta'addanci , kamar yadda hukumar yada labarai ta kasar Iran ta shaida.

Kafar watsa labarai ta Ahlul Bayt ta ruwaito cewa shugaban Nigeria Muhammadu Buhari yayi tattaunawa ta wayar tangaraho ta takwaransa na Saudi Arabia, Salman bin Abdul Aziz Al Saud.

A yayin tattaunawar, dukkan shugabannin guda biyu sun mayar da hankali ne kan muhimman alamura da suka shafi alaka tsakanin kasa-da-kasa, gami da harkokin da ke faruwa a fadin kasashen guda biyu.


(Labarin Cikakkun... | 2219 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

TOHFAH! YANZU AN 'KYALE GENERAL BURATAI AN DAWO KAN 'YAN SALAFIYYAH!
(Labarin Cikakkun... | 1311 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

TOHFAH! YANZU AN 'KYALE GENERAL BURATAI AN DAWO KAN 'YAN SALAFIYYAH!

HABA 'YAN SHI'A, WAI ME YASA KUKE MANA 'KARYA NE? A SHEKARUN BAYA KUNJE KUNYI HAYANIYA DA FADAWAN SARKIN ZAZZAU SAI KUKA ZUQE KUKA CE 'YAN SALAFIYYAH NE. YANZU KUMA FA'DANKU DA KUKA YI DA 'YAN'DARIKA KUN ZU'KE KUNCE DA 'YAN SALAFIYYAH NE KUKA YI. SABODA HAKA KU SAURARI MARTANIN DARUUL HADEETHIS SALAFIYYAH A JARIDAR DAILY TRUST DAZA TA FITO RANAR JIBI RANAR TALATA.

Mu Ahlussunnah yan Salafiyyah aikin mu shine karantar da Qur'ani da hadisan manzon Allah (SAW) a bisa fahimtar magabata na 'kwarai. Bamu da wani aiki inba wannan ba.


(Labarin Cikakkun... | 1311 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

SHIN RAGOWAR ''YA''YAN NASA BA AHLUL-BAITI BANE (003) ?
(Labarin Cikakkun... | 2163 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

SHIN RAGOWAR "YA"YAN NASA BA AHLUL-BAITI BANE (003) ?

SHUBUHOHIN SHI'A AKAN HADISIN MAYAFI DA WARWARE SU A BISA FAHIMTAR MALAMAI NA KWARAI.

4) Ga wata tambaya ga "yan shi'a:

menene hukuncin ragowar "ya"yan manzon Allah s.a.w da jikokinsa, shin su ba ahlul-baiti bane? Menene hukuncin ragowar yan uwan s.

Aliyu, ja'afar Akilu r.a ?

Menene hukuncin Nana khadija r.a suma duk ba ahlul-baiti bane?

Idan yan shi'a suka ce suma ahlul-baiti ne. Sai muce to ai suma basa acikin wadanda manzon Allah s.a.w ya lullube da mayafin, ta yaya suka zama ahlul-baiti ? idan yan shi'a suka ce manzon Allah s.a.w baikiraye su bane saboda galibin su basanan.


(Labarin Cikakkun... | 2163 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com