Muhawara Hausa
 

 
Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan kammalalliyar godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa; muna neman taimakonSa; muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu; wanda duk Allah Ya shiryar, to shi ne shiryayye, wanda duk Allah Ya batar, to ba mai shiryarwa a gare shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai ba Shi da abokin tarayya; ina shaidawa, hakika, Annabi Muhammadu Bawan Allah ne kuma ManzonSa ne (SAW).

Bayan haka dan tsokaci ne nake son yi kan sharuddan da suka kamata mutum ya lura da su kafin ya kafirta wani, kuma akwai bukatar a mayar da hankali sosai don ganin an nisanci aiwatar da abin da ba a sani ba, ko ba a fahimce shi ba sosai a sha'anin addini. Allah Ya ba mu dacewa.

Wannan rubutu ne da aka tsakuro daga makalar da marigayi Gambo Bako Malumfashi, Allah Ya jikansa Ya kuma gafarta masa, ya yi, dangane da mas'alar kafirci, kodayake har yanzu ba a wallafa littafin ba:

Mas'alar kafirtawa, mas'ala ce mai girma, kuma mai hadarin gaske, wadda ta dalilinta ne rarrabuwa da kiyayya da kashe-kashe tsakanin Musulmi suka auku. Don haka ya zama wajibi mutum ya yi tsantseni wajen fahimtar shiryarwa ta Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a kan wannan mas'ala.

Hadarin kafirta wani mutum ko tuhumar shi da kafirci, yana da yawa, sai dai saboda takaitawa zan ambaci kadan daga cikinsu:

(1) Ilimi

Lallai ne wanda zai kafirta wani ya zama mai ilimi, musamman ma a kan kashe-kashen kafircin da ake da su a karkashin maudu'in. Wannan kuwa wani al'amari ne da yake da bukatar a fahimce shi sosai ta yadda za a aiwatar da shi yadda ya dace. Dalilin wannan magana ta ilimi shi ne fadar Allah Madaukaki: "Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi. Lallai ne ji da gani da zuciya, dukkan wadancan, (mutum) ya kasance daga gare su, wanda ake tambaya ne." (k:17:36).

(2) Aiki ko magana

Lallai ne mai kafirtawar ya tsaya har sai mutumin da ake tuhumar (da kafircin) ya yi aiki ko maganar da za ta fitar da shi (daga da'irar) Musulunci ta hanyar furuci ko aiki ko rubutu ko nuni. Amma idan wani ne ya yi rubutun shi kuma ya karanta ko kuma bai ma san wanda ya rubuta ba, ko ba ya ma iya karanta abin da aka rubuta din, to wannan tuhumarsa cewa ya yarda da rubutun ko ya yi imani da shi, zalunci ne da zato wanda shari'a ta hana.

(3) Bayyanar kafirci

Lallai ne kafirci ya bayyana karara, wanda ba wata shubuha ta hanyar musanta wani abu wanda shari'a ta yi umurni da yin imani da shi, bayan sakankancewar umarnin shari'a ga wannan abin.

(4) Lallai ne mutumin (da ake son kafirtawa) ya kasance a kan ilmin abin da yake musawar, wato dole ne a koyar da shi kuma a bayyanar masa hujja da Alkur'ani da Hadisan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) wadanda ke nuna sabanin abin da yake a kansa.

Dalilin wannan shi ne fadar Allah Madaukaki: "Ba Mu kasance Muna yin azaba ba, har sai Mun aika Manzo." (k:17:15); da kuma fadar Allah Madaukaki: "Ka ce, to Allah Ne da hujja isasshiya… (aya)." (k:6:149).

Da kuma fadarSa Allah Madaukaki: "Kuma an yiwo wahayin wannan Alkur'ani domin in yi muku gargadi da shi da wanda labari ya kai gare shi…" (k:6: 19).

(5) Sauraro

Lallai a saurara, a ji amsar mutumin a kan hujjojin da aka kafa masa. Idan har ya yi shiru bai yi musu ba, to ya yarda ke nan, domin yin shiru yarda ne, amma idan ya zo da wasu hujjoji ko tawili wadanda ba su a kan hanya, to ba ya yiwuwa a kafirta shi, sai dai a yi ta yi masa bayani, har Allah Ya sa ya fahimta ta hanyar karantar da shi.

Amma idan ya yi musu kuma ba tare da wata hujja ba, ba tare da tawili ba, kuma ba tare da jahilci ba, wanda zai iya zama uzuri a gare shi, kuma ya bijire wa duk hujjojin da aka kawo masa domin zalunci da girman kai, wato ya siffantu da siffofin da Allah Ya ambace su inda Yake cewa, "Kuma suka yi musun sa, alhali zukatansu sun natsu da su domin zalunci da girman kai…" (k:27:14); to wannan ya kafirta, kafirci wanda ya fitar da shi daga (da'irar) Musulunci.

(6) Lallai a nemi tubarsa, (in har hakan ta kasance); za a nemi tubar tasa, ba tare da (ana) tsoratar da shi ba, (sai dai lallashi da nuni na shiryarwa) har zuwa kwana uku. Idan bai tuba ba, sai a kashe shi da takobi, saboda fadar Sayyiduna Umar (RA) cewa: "Don me ba ku tsare shi kwana uku ba, ku ciyar da shi kuma ku nemi tubarsa, ko ya tuba ya dawo ga umarnin Allah?" Muwadda Malik, Babi na 504, Hadisi na 1484.

Wadannan su ne sharuddan da suka kamata mutum ya lura da su kafin ya kafirta wani, wadanda suke da bukatar a fahimce su sosai kuma a yi kokarin aiwatar da su ta yadda ba za a kafirta mutum da wani aiki ko furuci ko rubutu ko abin da ya yi kama da shi a kan kuskure ba. Kowane lokaci ana son Musulmi, musamman mai wa'azin jan hankalin jama'a ya kasance yana yin taka tsantsan dangane da yadda yake gudanar da harkokinsa da jama'a, ta fuskar tausasawa da saukakawa.

Allah Ya yi mana muwafaka da abin da yake daidai. Wassalamu alaikum wa rahmatullah.

 Posted By Aka Sanya A Saturday, October 12 @ 15:50:37 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

"Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com