Muhawara Hausa
 

 
Yadda Musulunci ya 'yanta mace (4)
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Yadda Musulunci ya 'yanta mace (4)

4 – 10. Runtse ido da tsare farji da sauransu:

Manufar shari'ar Musulunci ita ce kare martabar mace wadda ita ce ginshikin iyali. Kuma kare martabarta zai tabbata ne kawai idan aka hana abin da zai kai ga yaduwar zinace-zinace. Zinace-zinace kuwa masominsu shi ne gwamutsuwar maza da mata da bayyana kawa da kallo a karshe kuma a auka wa keta martabar mace. Musulunci ya umarci maza da mata su runtse daga ganinsu kuma su tsare farjojinsu daga aikata zina. (k:24:30-31)

Musulunci ya hana mata bayyana ado ko kawarsu face ga mazansu da wadansu da shari'a ta ambata. (k:24:31). duk wadda ta yi tawaye ga wannan doka sai mu ajiye ta a sahun mushirikai da kafiran Yamma.

Musulunci ya hana mata sassautar da magana ga mazan da ba na su ba don kada su ba masu muguwar zuciyar damar su yi tsammanin wani abu daga gare su. "Ya matan Annabi! Ba ku zama kamar kowa daga (sauran) mata ba in kuka yi takawa, saboda haka kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cuta a zuciyarsa ya yi tsammani…" (k:33:32). Musulunci ya haramta kebanta da ajaniba ko yin tafiya ga mace ba tare da muharraminta ba. An karbo daga Ibn Abbas (RA) ya ce: "Na ji Annabi (SAW) yana huduba yana cewa: "Kada namiji ya kebanta da mace face tare da ita akwai muharraminta, kuma kada mace ta yi tafiya sai tare da muharrami." Sai wani mutum ya tashi ya ce: "Ya Manzon Allah! Lallai matata ta tafi aikin Hajji, ni kuma an rubuta ni cikin masu tafiya yaki kaza da kaza." Sai (SAW) ya ce: "Tashi ka tafi aikin Hajji tare da matarka." (Buhari da Muslim). Ibn Hajrin ya ce, "A cikinsa (Hadisin) akwai hanin kebanta da ba'ajanabiya kuma shi ne ijma'in malamai." (Fathul Bari: 4/92). Alkali Iyal ya ce, "Mace fitina ce kuma an hana kadaita da ita ce, saboda abin da aka halicci zukatan maza na sha'awa a kansu (mata), kuma aka sallada Shaidan a tsakaninsu…." (Ikmalul Mu'allim: 4/448). Haka Musulunci ya hana shiga gidan da mace take ba tare da muharraminta ba. Ukbatu bin Amir (RA) ya ruwaito cewa: "Manzon Allah ya ce: "Kashedinku da shiga gidajen mata!" Sai wani mutum daga Ansar ya ce: "Ya Manzon Allah koda matan dan uwa ne (wa ko kane)?" Sai (SAW) ya ce: "Matan dan uwa mutuwa ce!" Khurdabi ya ce: "Fadinsa matar dan uwa mutuwa ce" na nufin shigarsa gidan matar dan uwansa yana kama da mutuwa wajen ki da barna. Wato abin haramtawa ne. An kai iyaka ne wajen gargadi aka kwatanta da mutuwa…. (Almufham:4/501).

Musulunci ya hana mata cudanya da maza hatta a wuraren ibada. Abu Huraira (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Mafi alherin sahun maza, farkonsa, kuma mafi muninsa na karshensa. Mafi alherin sahun mata na karshe, mafi muninsa na farkonsa." (Muslim).

Khurdabi ya ce: "Sahun farko na mata ya kasance mai muni ne saboda kusancin numfashin maza da matan, hakika ana jin tsoron kada mace ta karkatar da hankalin namji ko namiji ya dauke hankalin mace." (Almufham).

Bayan bayani kan wannan Hadisi Sheikh Bin Baz ya ce: "Ya kasance ana umartar maza a zamaninsa (SAW) su jinkirta fita daga masallaci har sai mata sun idar da Sallah sun fice daga masallacin domin kada su rika cudanya da juna a kofofin masallaci duk da cewa dukansu suna da karfun imani da takawa. To yaya lamarin zai kasance ga wadanda suka zo a bayansu?" (Hukmul Ikhtiladi fi Ta'alim da Mujallar Albuhusul Islamiyya adadi na 15 ta shekarar 1406 Hijiriyya).

Musulunci ya tsananta haramcin fitar mace sanye da turare. Abu Musa Al-Ash'ari (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "duk matar da ta sanya turare ta fita a kan maza don su ji kanshinta to ita mazinaciya ce." (Abu dauda da Tirmizi da Nisa'i).

11. Kishin mata:

Wani muhimmin abu da makiya Musulunci suke kokarin ganin sun raba Musulmi da shi, shi ne na nuna kishi ga mata. Suna son Musulmi ya dauki matarsa kamar wata haja ta nuna wa mutane kyawunta, ya zama ba ya kishinta, ya bar ta kamar ungulu kazar kowa! Ba ya damuwa da ina ta je, ina za ta je, ina ta fito, kuma su wane ne abokan huldarta? A'a shi da ita daidai suke, kowa ya fita inda ya ga dama, ya hadu da duk wanda yake so ya yi mu'amalar da yake so da su! Wannan dabi'a ta rashin nuna kishin mata, dabi'a ce ta Turawan Yamma wadda take kaiwa ga yaduwar fasikanci da zinace-zinace da sauran ayyukan fasadi da barna. Kuma a kanta ce galibi ake samun rigima a tsakanin Musulunci da tunanin dan Adam da kuma tsakanin Musulmi da makiya Musulunci. Rigakafin da Musulunci ya yi don kare martabar mace a wannan bangare don kare ta daga shiga hannun miyagu, shi ne Turawa da 'yan korensu suke ganin gidadanci ne da ci baya. Kuma a kan haka ne suke sukar Musulunci da Musulmi.

Sheikh Muhammad Ahmad Al-Mukaddam ya ce: "Lallai daga cikin alamun girmamawar da Musulunci ya yi ga mace akwai abin da ya shuka a cikin zukatan Musulmi na nuna kishi a kansu. Abin da ake nufi da kishi, shi ne dabi'ar nan da take tunkuda namiji ya kare mace daga duk wani haramtaccen abu da kazanta da kuma abin kunya. Kuma Musulunci yana kirga kare mutunci da nuna kishi wajen kare iyali a matsayin jihadi da ake iya zubar da jini a kansa, a sadaukar da rai a tafarkinsa a kuma kirga wanda ya yi hakan a cikin masu samun darajar shahidai a gidan Aljanna. An karbo daga Sa'id dan Zaid (RA) ya ce: "Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: "Wanda aka kashe shi a kan kare dukiyarsa ya yi shahada, wanda aka kashe shi a kan kare jininsa ya yi shahada, wanda aka kashe shi a kan kare addininsa ya yi shahada, wanda aka kashe shi a kan kare iyalinsa ya yi shahada." Ahmad da Abu dauda da Tirmizi da Ibnu majah suka ruwaito. Kai Musulunci ma yana daukar kishi a kan mace daya ne daga cikin alamun imani. duk wanda ba ya kishin matarsa ba ya da imani, don haka ne Manzon Allah (SAW) ya kasance mafi kishin halitta a kan sauran al'umma. An karbo daga Mughira bn Shu'uba (RA), ya ce: "Sa'ad bin Ubbadah ya ce: "da zan ga wani namiji tare da matata da na sare shi da takobi ba tare da sassauci ba. Sai hakan ya isa ga Manzon Allah (SAW), sai ya ce: "Shin kuna jin mamakin kishin Sa'ad ne? Wallahi ni na fi shi kishi, kuma Allah Ya fi ni kishi. Yana daga cikin kishin Allah da Ya haramta alfasha abin da ya bayyana gada gare ta da abin da ya boyu." (Buhari da Muslim). Kuma an karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Lallai Allah Yana kishi, kuma lallai mumini yana kishi. Kishin Allah (na motsawa ne) in mumini ya aikata abin da Allah Ya haramta." (Buhari da Muslim). Kuma yana daga cikin kishi abin yabo a ga masoyi yana adawa wani ya yi tarayya da shi a cikin abin sonsa. don haka ne kishi yake da wasu na'o'in tasiri da babu makawa su taimaka wajen tsare martaba da mutunci, kuma shi ne yake yin tasiri wajen nuna hamayya da tsarewa da bayar da kariya ga abin da ake son, duk wanda ba ya da hamayya ba zai tsare matrabar iyalinsa ba.

Mutumin da ba ya da kishi shi ake kira da Larabci da duyus, wato mai tabbatar da kazanta a cikin iyalinsa, wato mutum ya zamo gaso-rogo ko mijin Hajiya, babu ruwansa da masu shiga kan iyalinsa ko masu hulda da su. Malamai sun ce: "duyus shi ne wanda ba ya kishin iyalin gidansa, kuma an samu gargadi mai tsanani tare da yi masa tattalin azaba a kan haka. An karbo daga Abdullahi dan Umar (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Mutum uku Allah Madaukaki ba zai dube su (da idon rahama) ba a Ranar Alkiyama: Mai guje (saba) wa iyayensa da mace mai shigar maza da kuma duyus (namiji marar kishin matarsa)" (Ahmad da Nisa'i suka ruwaito).

 Posted By Aka Sanya A Monday, September 09 @ 01:58:22 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

"Yadda Musulunci ya 'yanta mace (4)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com