Muhawara Hausa
 

 
Sallar Idi da ladubbanta
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi Sallar Idi da ladubbanta

Malamai sun hadu cewa ta kowane hali a ranakun Idi biyu a hana yin azumi, koda na bakance ko kaffara kamar yadda Annawawi ya nakalto a sharhinsa ga Sahihu Muslim. (8/15). Kuma sun ce, hikimar hanin ita ce idan aka yi azumin kamar an ki amincewa da liyafar da Allah Ya shirya ga bayinSa ne. (Nilul Audar, 4/262).

Sannan Sunnah ce, a yi wanka a sanya sababbin kaya ko a wanke wanda suka fi kyau cikin tufafin mutum, a sa turare a fita masallacin Idi, maza da mata manya da yara tare da tsare ladubban fitar, wato kada mata sun caba ado ko sun sanya turare kuma kada a cakuda maza da mata da sauran abubuwan da shari'a ta hana.

Ranar Sallah ranar ce ta murna da farin ciki da bukukuwa, to, sai dai kada wajen murna a wuce gona da iri. Kada murna ta sanya a koma ga sabo. Kada murna ta sa a aikata bidi'o'in da za su bata kyawawan ayyuka.

Daga cikin ladubban murnar Sallah akwai:

1. Taya juna murna da duk lafazin da ya sauwaka, kamar "Allah Ya karba mana da makamancin haka. An ruwaito cewa wasu daga magabatan kwarai sun aikata haka. Misali Jubairu bin Nufair ya ce, "Sahabban Annabi (SAW) idan suka hadu da juna sukan ce, "Allah Ya karba mana, Ya karba muku." Imam Ahmad ya ce Isnadinsa mai kyau ne, sannan Hafiz ya kyautata Isnadinsa a cikin Fathul Bari (2/517), kuma a duba Tamamul Minnah na Albani don karin bayani. Kuma an ruwaito Imam Ahmad yana cewa: "Ba zan fara fada wa mutum haka ba, amma idan ya fada min zan amsa." Shi kuma Shaihul Islam Ibnu Taimiyya (RH) ya ce, "Fara taya murna ba Sunnah ce da aka yi umrni da ita ba, kuma ba a hana ba, wanda ya aikata, ya yi koyi, wanda ya ki, ya yi koyi." Majmu'u Al Fatawa (24/253). Hakika irin wannan gaisuwa na yin tasiri wajen karfafa zumunta da ruhin soyayya a tsakanin Musulmi.

2. Ziyartar 'yan uwa da makusanta da sada zumunta. Wannan mustahabbi ne a kowane lokaci, amma an fi karfafa shi a irin wannan lokaci, musamman ziyartar iyaye, domin ana sanya musu farin ciki, kuma haka cikar umarnin Allah ne na a kyautata musu.

3. Wadata abinci da abin sha: Babu laifi a wadata abinci da abin sha a wadannan ranaku ba tare da almubzzaranci ba. Kuma ya hallata a yi wasannin da suke halal, saboda Hadisin Anas a wurin Abu Dauda da Nisa'i bisa Isnadi ingantacce da ya ce: "Lokacin da Annabi (SAW) ya isa Madina, ya iske su suna taruwa rana idoji, sai ya ce, "Kuna da wuni biyu da kuke wasanni a cikinsu, to, hakika Allah Ya musanya muku da mafiya alheri: Ranar karamar Sallah da Ranar Layya." Kuma ya halatta a yi wake-waken da suka halatta, saboda Hadisin A'isha (RA) cewa, "Manzon Allah (SAW) ya shiga wurina ina tare da wasu kuyangi biyu suna kida da waka (wasu sun ce da shantu) sai ya kishingida a kan tabarma ya juya fuskarsa. Sai Abubakar ya shigo ya yi min fada ya ce "Shaidan a gidan Annabi (SAW)? Sai Manzon Allah (SAW) ya kalle shi ya ce "kyale su- a wata ruwayar ya ce "Ya Abubakar ko wadanne mutane suna da Idi, wannan Idinmu ne."

Wasu bidi'o'i da ake yi lokacin bukukuwan Idi:

1. Wasu kan kirkiro ayyuka na raya daren Idi da ibada bisa dogaro da Hadisan da ko dai masu rauni ne ko na karya.

2. Ziyartar makabarta, wannan ya saba wa manufar Idi na nuna farin ciki da jin dadi, domin a cikin zuwa makabarta akwai jaddada bakin ciki, kuma hakan ya saba wa shiriyar Manzon Allah (SAW) da ayyukan magabatan kwarai.

3. Cudanya tsakanin maza da mata a lokutan bukukuwan. Wannan babbar fitina ce, mai hadari da ya wajaba shugabanni da malamai su hana, kuma ya kamata Musulmi manya da matasa su rika jira mata su bar masallatai kafin su tashi bayan idar da Sallah.

4. Fitar mata sanye da turare cikin ado: Wajibi ne mahaifa da waliyan mata su rika umartar su da suturce jiki da sanya hijabi da lizimtar ladubban fita daga gida tare da gargadinsu kan auka wa abin da zai fusata Allah. Idan ba za su tsare hukunce-hukuncen shari'a ba, to, wajibi ne su hana su fita gaba daya.

5. Sauraren haramtattun kade-kade da wake-wake, kila wasu na iya fakewa da Hadisin kuyangi biyu su aikata abin da yake haram. Manzon Allah (SAW) ya ce, "Za a samu wasu mutane a cikin al'ummata da za su rika halatta zina da alhariri da giya da wake-wake da kayan kade-kade." Don haka wajibi ne a guje wa wake-wake da kade-kaden da suka saba wa shari'a.

6. Babban abin bakin ciki shi ne mutane da yawa suna wasa da Sallah cikin jama'a ko su yi barci ba su yi sallar ba, saboda sun bata lokacinsu wurin hira ko wasanni sun gaji a ranakun Sallah.

Allah Ya Ka tabbatar da mu a kan imani da aiki nagari, Ka rayar da mu rayuwa mai tsabta, Ka riskar da mu ga salihai, Ka sanya iliminmu ya zamo don neman yadarKa da kusantarKa, mai amfanarwa ga bayinKa, Ka jibince mu a duniya da Lahira, Ka shiryar da mu zuwa ga gaskiya da izininKa, lallai Kai Kana shiryar da wanda Ka so zuwa ga tafarki madaidaici.

 Posted By Aka Sanya A Monday, September 09 @ 01:26:41 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

"Sallar Idi da ladubbanta" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com