Muhawara Hausa
 

 
Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, mun karanci bayanai kan ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu, to yau ga ci gaba daga manuniya ne kan:

Hanyoyin Kare Kai Daga Zina Da Luwadi Da Madigo

Saboda hikimar Ubangiji da rahamarSa, duk abin da Ya haramta wa bayi, to za a bude wata kofar da mutum zai biya bukatarsa ba tare da ya afka wa wancan abin da Allah Ya hana din ba. Wannan abu haka yake a nan ma, domin dai mun ji irin tarin illolin da suke tattare da yin zina da luwadi da madigo, to amma babu yadda namiji ko mace za su rayu ba tare da sun sami inda za su zubar da sha'awarsu idan ta taso ba, saboda haka sai Musulunci ya halatta wadannan abubuwa masu zuwa don kauce wa afkawa cikin zina:

1. AURE: Allah Madaukakin Sarki Ya halatta wa maza su auri mata, inda yake cewa: "To ku auri abin da kuke so na mata, bibbiyu (ko) uku-uku (ko) hurhudu. Idan kuwa kuna tsoron ba za ku iya adalci ba, to ku auri daya, ko kuma abin da damarku ta mallaka. Wannan shi ne abin da zai sa ba za ku karkace ba." (Annisa'i: 3).

Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) kuma yana cewa, "Ya ku taron samari, duk wanda ya sami iko (ma'ana zai iya rike mata) to ya yi aure, domin shi ne mafi abin da yake sa runtse ido, kuma mafi sawa a tsare farji. Duk kuwa wanda bai samu iko ba, to ya yi azumi, domin (shi azumi) kariya ne a gare shi." Bukhari da Muslim.

Wannan aya da hadisi suna nuna mana halaccin mutum ya yi aure, kuma ya auri matar da yake so, wadda ta kwanta masa a rai, matukar ba ta cikin wadanda Allah Ya haramta masa ya aura. Saboda haka da mazinata da 'yan luwadi da masu madigo za su yi tunani da sun ga yadda Musulunci ya sauwake musu hanya, ta hanyar su yi aure, sai ya zama duk abin da za su yi halal ne, in ma sun yi niyya Allah Ya ba su lada, kamar yadda hadisi ya nuna.

2. Mallakar bayi: Musulunci ya halatta wa namijin da ya mallaki baiwa ya yi sadaka da ita, don kare mutuncinsa da mutuncinta. Ko kuma ya ‘yanta ta ya aure ta.

3. Azumi: Yin azumi, kamar yadda hadisin da ya gabata ya nuna [wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito] kariya ne a gare shi, saboda (shi) mai azumi, an umarce shi da ya kare gabbansa daga barin haramun, kada ya yi aikin banza, ko maganar banza, ko kallon banza, wanda kuwa duk zai yi azumi ya kiyaye gabbansa daga wadannan abubuwa, to babu ko shakka Allah zai ba shi tabbata a kan da'arsa, ba zai kyale shi ga shaidan ba, har ya kai shi zuwa ga (aikata) haramun.

4. Nisantar Abubuwan da Suke Motsa Sha'awa: Ya zama mutum yana nisantar duk wani abin da zai motsa masa sha'awarsa har ya kai shi zuwa ga neman mata, ko luwadi, ko madigo, kamar kalle-kallen finafinan batsa, karanta mujallun banza, raye-raye tsakanin maza da mata, sauraron kide-kide da sauransu. Haka nan da nisantar wuraren da ake saba wa Allah, inda yake hada maza da mata, ana shedana da ayyukan banza.

5. Shagalta da ayyukan alheri: Duk wanda zai shagaltar da kansa (wajen gudanar) da ayyukan ibada da alheri, to ba zai sami lokacin da zai je zuwa ga zina ko luwadi ko madigo ba. Musulmi na hakika, ba shi da wani lokaci da zai tafiyar da shi wajen saba wa Allah, duk lokutansa na ibada ne da tsoron Allah.

6. Tsoron Allah a koyaushe: Kamar yadda Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce, "Ka ji tsoron Allah a duk inda kake".
kofar Tuba A Bude Take

Wani ko wata za iya tunanin cewa yanzu na ji wa'azi, to yaya zan yi in tuba in daina, kuma shin ma Allah zai karbi tuban nawa, bayan dukkan wadannan abubuwa da na aikata? Sai mu ce:

Babu wani zunubi a bayan kasa da Allah ba Ya gafarta shi, matukar dai mai yin sa ya tuba, tuba ingantacciya, saboda Allah Yana cewa, "Ka ce, ya ku bayiNa wadanda suka yi wa kansu barna kada ku debe kauna ga rahamar Allah, hakika Allah Yana gafarta zunubai gaba daya, lallai shi Allah, Mai gafara ne, Mai jinkai". (Surar Azzumar, aya ta 53). Sannan Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Allah Ya sanya wata kofa a wajen mafadar rana, fadinta tafiyar shekara saba'in ce, saboda tuba, ba kuma za a rufe wannan kofar ba, matukar dai rana ba ta bullo daga inda kofar take ba". Tirmizi ne ya rawaito wannan hadisi.

A wannan aya da hadisi, za mu ga yadda Allah Madaukakin Sarki, saboda rahamarSa da falalarSa, Ya bude tangamemiyar kofar karbar tuba, har zuwa lokacin tashin alkiyama. Don haka babu wani zunubi da mutum zai yi a fadin duniyar nan, face in ya tuba, Allah zai karbi tubansa. Abin da dai ya wajaba a kiyaye yayin tuban shi ne:

• Yin nadama a kan abin da ya gabata, ya zama yana tunawa kuma yana damuwa, yana nadama, yana jin yaya ma aka yi ya aikata wannan laifin!

• kudurcewa a zuciya yayin tuba, cewa ba zai kara koma wa wannan laifi ba, har karshen rayuwarsa.

• Barin wannan sabon, in yana cikin yi ne yayin da zai tuba, kada ya ce bari in karasa, sannan sai in tuba.

• Yin tuban a lokacin da Allah Yake karba, shi ne kafin tashin alkiyama, kuma ba lokacin da yake gargarar mutuwa ba. Hakika Allah ba Ya karbar tuba a wadannan lokatai guda biyu, kamar yadda Alkur'ani da hadisi suka nuna.

• Ya zama ya sauke nauyin wani da ya hau kansa, idan kudi ne ya biya shi, in cin mutunci ne ya nemi ya yafe masa.

Wadannan su ne abubuwan da mai tuba zai kiyaye da su yayin tubarsa. Allah Madaukakin Sarki Ya sa mu dace.

Ina So In Tuba Sai Dai…

Da yawa daga cikin mutane suna son su tuba su bar zunubin da suke yi, sai wasu abubuwa sukan zo su sha gabansu, su kange su ga barin tuba din, har kuma su halaka suna kan wannan sabon, to amma mutum musulmi, wanda ya san abin da yake, ya san babu wani abin da yake kare mutum daga tuba.

Mu kwana nan, sai mako na gaba mu karasa, in Allah Ya kai mu!

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 08 @ 23:50:10 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com