Muhawara Hausa
 

 
Idan za ku fadi magana ku yi adalci
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Idan za ku fadi magana ku yi adalci

Daga hudubar Imam Salah bin Muhammad Al-Budair

Masallacin Annabi, Madina

Godiya ta tabbata ga Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Ina shaidawa Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma ManzonSa ne. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku ji tsoron Allah, hakika wanda ya ji tsoron Allah ya tsira, wanda kuma ya bi son zuciya ya bata. "Ya ku wadanda suka yi imani ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa da takawa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa (Musulmi)." (k:3:102).

Ya ku Musulmi! Ku sani ana fassara maganar mutum bisa jahilci kuma a kafa masa hujja a kai. Kuma harshe yana da kaifi biyu kodai jahilci ya fi munanta shi, ko hankali ya rinjayar da shi. Kuma laifin magana barin yin adalci yayin furuci.

Wani mawaki ya ce: "Yin shiru ya fi yin furuci da zunubi. Ka kasance mai shiru ka kubuta, idan kuma za ka yi magana, to, ka yi adalci."

Kuma Allah Madaukaki Ya ce: "Kuma idan kun fadi magana, to, ku yi adalci, kuma koda ya kasance (a kan) ma'abucin zumunta ne." (k:6:152). Kuma Ya sake cewa: "Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wadansu mutane ta dauke ku a kan ba za ku yi adalci ba. Ku yi adalci. Shi ne mafi kusa ga takawa. Kuma ku bi Allah da takawa. Lallai Allah Masani ne ga abin da kuke aikatawa." (k:5:8).

Ka yi adalci koda an fusata ka, ka yi adalci koda ka yi fushi. Kada ka kasance wanda idan ba ya nan za a aibanta shi, idan kuma yana nan za a ci namansa a yawaita zaginsa a tsananta sukarsa.

Mutum mai girma abin kiyayewa, shi ne wanda ya kyautata harshensa ya lizimci hanyar gaskiya a furuncinsa, bai saba da karya a maganarsa ba. Kuma kiyayya da gaba da wadansu ba su dauke shi ga yin karya da kirkirar karya gare su ba. Fushi bai ingiza shi ya kirkiri karya ko ya yi ta'addanci ga wani.

Ya ku Musulmi! Sakin baki wajen cutar da wadansu da magana jahilci ne, sannan kirkirar karya zuma ce ta wawaye. Jin dadin yin karya dabi'ar fasikai ce, munantawa wajen tuhuma illa ce, kuma jifar mutane da kirkirarrun maganganu hanyar ma'abuta fajirci ce. Duk wanda ke da dabi'a abar zargi, mugun hali ya zame masa jiki, sai ya rika wuce gona da iri wajen cin mutuncin mutane. Ya rika halatta karya da shaidar zur don bata abokan aiki ko sana'arsa. Ya rika kaskantar da abokai da wadanda suka saba ga fahimta ko ra'ayinsa. Ya yi ta yin bakin fenti ga masu adawa da ra'ayi da fahimtarsa ta hanyar kirkira musu munanan abubuwa da jingina musu kazaman laifuffuka.

Ya ku Musulmi! Wanda ha'incinsa ya yi girma, makircinsa ya bayyana, sai ya rika yawaita yabo ga makusantansa da masu sam masa wani abu, ya yi sutura ga mai kin gaskiya, idan kyautar ta yanke ya yanke masa, sai yabon da yake yi masa ya koma cin zarafi, suturar da ya yi masa ta koma tsaraici, yabo ya koma zagi, addu'a ta koma la'ana. "Idan aka ba su daga cikinta (dukiya), su yarda, kuma idan ba a ba su ba daga cikinta, sai su zamo suna masu fushi." (k:9:58).

Ya ku Musulmi! Hasada da bakin ciki suna yawaita a tsakanin mutanen da aiki ko sana'a ko zama ya hada su. Sai su yi ta gaba da hassada, sashinsu ya rika bata mutuncin daya sashin ta hanyar suka da zagi da batanci da wulakanci da kaskantarwa, musamman idan aka samu sabani komai kankantarsa. Babu mai kubuta daga haka sai wanda takawa ta yi masa katanga, kuma hankali ya tsare shi.

Za ka ga mutane na nade maganganun abokan zama sashinsu ga sashi ba za su ruwaito su ba, su binne su ba za a watsa su ba, saboda sun auku ne a lokacin fushi da hassada. Sai mutum ya dauki adawa da 'yar kure da tsarkake kai da kulli su zamo dabi'unsa. Sai wuce iyaka da karin gishiri da karya da kirkirar karya da kaidi su shigo cikin al'amuransu.

Ibnu Abdulbar (Rahumahullah) ya ce, "Wallahi hakika mutane sun ketare iyaka wajen yin giba da zargi. Ba su tsaya kan zargin wani bangare kadai ba, sun hada da kowa, ba su tsaya ga zargin jahilai ba, sun hada da malamai. Wannan kuwa duk silarsa jahilci ne da hassada."

Imam Az-Zahbi (Rahimahullah) ya ce, "Maganganun batanci daga tsararrakin juna ba a kula shi, musamman idan ya bayyana maka an yi ne don adawa ko don mazhaba ko don hassada, kuma ba a kubuta daga hakan sai wanda Allah Ya tsare shi." Kuma ya sake cewa: "Galibi ba a kula da maganganun tsararraki, musamman idan akwai munakasha a tsakaninsu."

Don haka kashedinku daga bin muguwar hanya da ke zame duga-dugai ta gadar da nadama. Kashedinku – ya bayin Allah – daga shagala da watsa aibobi da bayyanar da laifuffukan wadansu da bin al'aurorinsu da gazawarsu da yi wa mutane karya da suka ko bata su, da bata sunansu domin wadansu dalilai na son zuciya mai umarni da mugun aiki.

Ku ciru daga munanta zato, ku nemi uzurori ga mutane, ku yafe laifuffuka da gazawarsu, kada ku bari Shaidan ya batar da ku, domin lallai shi makiyi ne mai batarwa mabayyani.

Ina fadin abin da kuke ji ina mai neman gafarar Allah a gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukkan zunubi da kuskure, ku nemi gafararSa, lallai Shi Mai gafartawa ne ga wadanda suka tuba suka koma gare shi.

Huduba ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Makagin halitta, Masanin abubuwan da suke boye. Ina gode maSa cikakkiyar godiya marar iyaka. Ina shaidawa babu wanda ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, kuma ina shaidawa lallai Annabinmu kuma Shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, zababbenSa, mai ganawa da Shi, kuma abin yardarSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa mamaya a addini, mamaya a yakini. Tsira da amincin Allah matabbata har zuwa Ranar Sakamako su tabbata a gare su.

Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku bi Allah da takawa domin yi maSa takawa shi mafi falalar abin nema, kuma yi maSa da'a ita ce mafi daukakar nasaba. "Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa kuma ku fadi magana wadda take daidai. Sai Ya gyara muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya yi da'a ga Allah da ManzonSa, hakika ya rabauta da rabo mai girma." (Ahzabi: 71-72).

Ya ku Musulmi! Babu abin da yake maganin wawa, irin yin hakuri, kuma babu abin da yake maganin jahili irin shiru. Idan ka yi shiru ga jahili hakika ya ishe shi jawabi, kuma ya ishe shi ukuba. Kuma babu hutu face ta yin afuwa da danne zuciya. Hakika an ce: "A cikin danne zuciyarka akwai hutu gare ka." Al-Ahnaf Bin kais ya ce: "Babu wani da zai yi gaba da ni face na kama shi a cikin al'amrinsa da halaye uku: Idan yana sama da ni, sai in ba shi girmansa, idan yana kasa da ni sai in daukaka matsayinsa; idan kuma tsarana ne sai in samu daukaka a kansa."

Domin haka ku yi afuwa ku yi yafiya. Ku tuna da ladar afuwa da sakamakon yafiya da akibar hakuri. Ku guji abin da zai raunana karfinku ko ya rarraba kanku.

Ku yi salati da taslimi a bisa mai shiryar mafificin halitta (SAW).

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 08 @ 23:39:18 PDT Da MediaHausaTeam
 

Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin AbokiYa Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

"Idan za ku fadi magana ku yi adalci" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama

Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com