Muhawara Hausa
 

 

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

It's Haram To Aid, Promote Or Participate In The Oodua Nation Agitation
(Labarin Cikakkun... | 2035 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
(Labarin Cikakkun... | 2035 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tauhidi ginshikin Musulunci (5)
(Labarin Cikakkun... | 6053 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tauhidi ginshikin Musulunci (5)

Ba zan iya amfana muku komai a wajen Allah ba". Sai ya kira Abbas (xan baffansa) ya ce, "Ba zan iya amfana maka komai a wajen Allah ba". Sai ya kira Safiyya (‘yar uwar mahaifiyarsa) ya ce, "Ba zan iya amfanar maki komai wajen Allah ba". karshe kuma sai ya kira 'yarsa ya ce, "Ya Fatima, idan kina da bukata ta dukiya, ki tambaye ni abin da kike so. Idan ina da shi zan ba ki, amma ba zan iya amfana miki komai wajen Allah ba."

BABI NA GOMA SHA SHIDA

Abin da ke faruwa ga Mala'iku Idan Allah ya yi magana Idan Allah (S.W.T) Ya yi magana Mala'iku sukan tsorata har ma su suma. Domin haka ne Allah Ya ba da labari a cikin Suratul-Saba, "Idan aka zare wannan tsoron daga zukatansu (Mala'iku) sai su ce wa Jibrilu, ‘me Ubangji Ya faxa?" Sai Jibrilu ya ce ‘Allah Ya faxi gaskiya, domin Shi Maxaukaki ne, Mai Girma".

An samu Hadisi daga Abu Huraira, Annabi (S.A.W) ya ce, "Idan Allah Ya hukunta wani al'amari a sama, Mala'iku sai su faxi da fukafukansu don kaskantar da kai ga zancen Allah domin suna jin maganar kamar wata sarka ce aka ja a kan falalen dutse. Wannan karar tana sanya su suma har idan suka farka daga wannan sumar sai su ce ‘me ubangijinmu Ya faxa?" Sai Jibrilu ya ce, ‘Allah Ya faxi gaskiya domin Shi ne Maxaukaki, Mai Girma'. To a wannan lokaci ne aljannu masu satar ji suke satar ji, kuma su faxa wa na kusa da su. Har ma lokacin da Sufwan yake siffantawa sai ya buxe tsakanin yatsunsa, wani a kan wani ya ce haka suke yi. Watau na sama ya faxawa na kasa da shi har su faxa wa boka ko xan duba. Shi kuma idan ya tashi zai faxa sai ya kara karya xari.


(Labarin Cikakkun... | 6053 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tauhidi ginshikin Musulunci (4)
(Labarin Cikakkun... | 11932 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tauhidi ginshikin Musulunci (4)

Babi na Goma Sha daya

Ba a yanka domin Allah a wurin da ake yanka domin wanin Allah

Allah Ya ce, "kar ka je ka yi sallah a wannan masallacin har abada, domin masallacin da aka gina shi a kan tsoron Allah tun ranar gininsa shi ya fi dacewa ka yi sallah a ciki domin akwai mazaje muminai a cikinsa wadanda ke kaunar su tsarkaka. Allah kuma Yana son masu son tsarkakuwa." (Taubah, 108) 8

Babi na Goma Sha Biyu

Shirka ne yin alwashi domin wanin Allah

Allah Ya ce, dagane da sha'anin muminai, "Su ne wadanda suke cika alwashinsu, kuma suna tsoron wata rana wacce take sharrinta mai fantsama ne". (Al-Insan, 7). Amma awata aya sai Allah Ya ce, "Duk abin da kuke ciyarwa ko kuka yi alwashin bakance, hakika Allah masani ne a kansa." (Bakara, 270).

An samu Hadisi daga A'isha (R.A) cewa Annabi (S.A.W) ya ce, "Wanda ya yi alwashin zai bi Allah to ya yi kok arin daurewa domin biyayaya ga Allah. Amma wanda yayi alkawarin zai sabawa Allah, to ya bari kar ya sabawa Allah din".


(Labarin Cikakkun... | 11932 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Musulmi da farfagandar makiya
(Labarin Cikakkun... | 7385 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Musulmi da farfagandar makiya

Masallacin Haramin Ka'aba da ke Makka

Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da aminci su tabbata ga Annabi (SAW).

Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku bi Allah Madaukaki da takawa ku sani bin Allah da takawa shi ne zai kare mu daga dukan bala'o'i.

'Yan uwa a imani! Tun lokacin da Allah Ya halicci duniya ake fafata yaki a tsakanin sassa daban-daban domin a mallake zukata da tunanin mutane; kamar yadda ake neman mallakar dan Adam a jikinsa. A yau ana yakar dan Adam ta wajen tunani da fikirarsa fiye da kowane lokaci; ana yakar tunaninsa ta dukan hanyoyi fiye da yaki irin na soja. Wannan yaki, shi ne yakin farfaganda.

Farfaganda wata muguwar hanya ce, kuma makami mafi hadari da ya fi ruguza dan Adam. Hadarinta babba ne kuma ba za a iya misalta barnarta ga dan Adam ba, saboda mugun illarta. Don haka wajibi ne a samu yunkuri don nazartarta ta yadda za a gano tushenta a tuttuge ta, kafin ta jawo mummunar illar da ba za a iya magance ta ba ga dan Adam.

'Yan uwa a Musulunci! Idan dayanmu zai yi dubi na basira ga tarihin dan Adam, zai ga cewa farfaganda da jita-jita sun taka rawa da tasiri a dukan zamunna; bilhasali ma sun samu gurbi babba wajen ci gaban masu da'awar wayewa, kuma su suke jawo rudu da bala'o'i ga kasashe da dama. An bi dukan matakan shigar da wannan muguwar dabi'a, domin juya akalar duniya kafin bayyanar Musulunci. Musulunci a matsayinsa na addinin da ginshikinsa shi ne tabbatar da rahama da adalci da zaman lafiya ga dan Adam, ya dauki kwararan matakai don yaki da wannan muguwar dabi'a, ta hanyar bin matakan haramta ta a cikin Alkur'ani da Sunnah.


(Labarin Cikakkun... | 7385 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tauhidi ginshikin Musulunci (2) - (3)
(Labarin Cikakkun... | 6784 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tauhidi ginshikin Musulunci (3)

Sanya kambu da guru da laya da makamantansu don dauke wata cuta ko tunkudeta, shirka ne Allah Ya ce, "Ku b ani labarin abin da kuke kira ba Allah ba, yanzu idan Allah Ya nufe ni da wani ciwo za su iya warkar da ni, ko Allah Ya nufe ni da wata rahama da za ta same ni, shin za su tare wannan rahamar ba za ta same ni ba? To ka ce, ni dai Allah ne madogara na kuma gareShi duk masu dogara suke dogara." (Zumar, 38).

An ruwaito daga Imrana dan Husaini (R.A) ya ce, Annabi (S.A.W) ya ga wani mutum sanye da kambu na farin karfe sai Annabi ya ce, "mene ne wannan?" Sai ya ce ai maganin shawara ne. Sai Annabi ya ce, "To cire ta, ba za ta kara maka komai ba sai rauni. Kuma wallahi da ka mutu da wannan kambun a jikinka da ba ka da rabo har abada." (Imam Ahmad ya ruwaito).

An samu wani Hadisi daga Ukbata dan Amru shi kuma ya karbo daga Annabi (S.A.W). Annabi ya ce, "Wanda ya rataya laya, to kar Allah ya biya masa bukatarsa. Wanda kuma ya rataya wuri, kar Allah Ya yi masa maganin abin da ya rataya dominsa". A wata ruwaya Annabi cewa ya yi, "Duk wanda ya rataya laya to ya yi shirka da Allah" kamar yadda aka samu daga Abi Hatim shi kuma daga Huzaifa; wata rana ya ga wani mutum yana sanye da zare wanda aka yi guru da shi wai maganin zazzabi, sai ya tsinke wannan zaren, sai ya karanta masa ayar Al-kur'ani inda Allah Yake cewa, "Yawancin wadanda suka yi imani da Allah sai a same su kuma suna shirka da Allah." (Yusuf, 106).


(Labarin Cikakkun... | 6784 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
(Labarin Cikakkun... | 5194 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan kammalalliyar godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa; muna neman taimakonSa; muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu; wanda duk Allah Ya shiryar, to shi ne shiryayye, wanda duk Allah Ya batar, to ba mai shiryarwa a gare shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai ba Shi da abokin tarayya; ina shaidawa, hakika, Annabi Muhammadu Bawan Allah ne kuma ManzonSa ne (SAW).

Bayan haka dan tsokaci ne nake son yi kan sharuddan da suka kamata mutum ya lura da su kafin ya kafirta wani, kuma akwai bukatar a mayar da hankali sosai don ganin an nisanci aiwatar da abin da ba a sani ba, ko ba a fahimce shi ba sosai a sha'anin addini. Allah Ya ba mu dacewa.

Wannan rubutu ne da aka tsakuro daga makalar da marigayi Gambo Bako Malumfashi, Allah Ya jikansa Ya kuma gafarta masa, ya yi, dangane da mas'alar kafirci, kodayake har yanzu ba a wallafa littafin ba:

Mas'alar kafirtawa, mas'ala ce mai girma, kuma mai hadarin gaske, wadda ta dalilinta ne rarrabuwa da kiyayya da kashe-kashe tsakanin Musulmi suka auku. Don haka ya zama wajibi mutum ya yi tsantseni wajen fahimtar shiryarwa ta Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a kan wannan mas'ala.


(Labarin Cikakkun... | 5194 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (1)
(Labarin Cikakkun... | 7634 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (1)

Huduba ta Farko:

Hamdala da Taslimi da Mukaddima:

Bayan haka! Ya ku bayin Allah! A 'yan kwanakin nan Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi (Hafizahullah) ya yi rubutu da tsokaci game da siyasar Najeriya, inda ya ba da shawarwari da nasihohin da za su kawo wa kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya yi kira tare da jan hankali ga manyan jam'iyyun siyasar kasar nan wato PDP da APC da wasu daga cikin 'yan takararsu, Janar Buhari da Shugaba Jonathan cewa, domin maslahar Najeriya, ya kamata Janar Buhari da Shugaba Jonathan su hakura da takara. Domin takararsu na iya jefa Najeriya cikin hadari na tashin hankali da rudani. Ya kawo dalilansa na yin tsokacin da har ya kai ga rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Janar Buhari da Shugaba Jonathan. To, amma fitar wannan bayani ke da wuya, sai wasu magoya bayan Janar Buhari da wasu mabiya son zuciya suka yi ca a kan Malam, mai zagi na yi, mai zambo na yi, mai habaici na yi. Har da masu tsinuwa da la'ana duk na gani kuma na karanta kuma na saurare su. Ba ma wannan kadai ba, wasu marasa kunya har cewa suka yi wai Sheikh Ahmad Gumi sai da ya sha ya bugu sannan ya rubuta wannan wasika zuwa ga Janar Buhari. Wasu kuma har tsagerancinsu da rashin tarbiyyar ya kai su ga cewa wai, Dokta Ahmad ba dan Sheikh Abubakar Gumi ba ne na halak. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Wannan wane irin zance ne na jahilci? Wannan wace irin al'umma ce muke rayuwa a cikinta da ba ta san inda ke yi mata ciwo ba?

Ya ku bayin Allah! In takaice muku labari, wallahi a cikinsu har da masu cewa wai Atiku ne ko Kwankwaso ko PDP ko Yahudawa ne suka saye Malam ya yi musu aiki. Da masu cewa wai, kuskure ne malamai su tsoma baki cikin siyasa, kamata ya yi su zuba ido su yi kallo su kame bakinsu game da siyasar kasar nan. Maganganu iri-iri na shirme da wawanci wallahi da ka saurare su, ka san mai yin su kodai jahili ne, ko mabiyin son zuciya.


(Labarin Cikakkun... | 7634 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

Sabuwar Shekarar 1439 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi (2)
(Labarin Cikakkun... | 6369 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Sabuwar Shekarar 1439 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi (2)

Bayyanar Musulunci ke da wuya sai watanni masu alfarma suka koma kamar yadda suke a farkon halitta inda Allah Madaukakin Sarki Ya haramta wannan al'ada ta jinkirtawar cikin fadinSa: "Lallai ne kidayayyun watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne a cikin Littafin Allah a ranar da Ya halicci sammai da kasa daga cikinsu akwai hudu masu alfarma. Wannan shi ne addini madaidaici. Saboda haka kada ku zalunci kanku a cikinsu. Kuma ku yaki mushirikai gaba daya kamar yadda suke yakar ku gaba daya. Kuma ku sani cewa lallai ne Allah Yana tare da masu takawa. Abin sanni kawai "Jinkirtawa" kari ne a cikin kafirci ana batar da wadanda suka kafirta game da shi: suna halattar da wata a wata shekara kuma su haramta da shi a wata shekarar domin su dace da adadin abin da Allah Ya haramta. Saboda haka suna halattar da abin da Allah Ya haramtar. An kawace musu munanan ayyukansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai." (k:36-37).

Kuma Ma'aiki (SAW) a Hajjinsa na Ban-Kwana ya ce, "Ku saurara! Lallai zamani ya juyo kamar yadda Allah Ya tsara shi a ranar da Ya halicci sammai da kasa,(1) shekara wata goma sha biyu ne; hudu daga cikinsu masu alfarma ne. Uku suna jere – Zul-kida da Zul Hajji da Muharram; na hudun shi ne Rajab na Mudar, wanda yake zuwa a tsakanin Jimada Akhir da Sha'aban." Wato yana nufin cewa sunayen watanni sun komo kamar yadda suke a farkon halitta, kafin al'adu su shigo su jirkita su. Kuma ga shi an haramta amfani da al'adar nan ta jinkirtar wani wata don ya fada wata shekara bayan tsawon zamani da aka share ana yi a matsayin abin da mutane suka yi imani da shi tare da mayar da shi addini kaka da kakanni.

Yadda aka fara kidayar shekarar Musulunci:


(Labarin Cikakkun... | 6369 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tauhidi ginshikin Musulunci (1)
(Labarin Cikakkun... | 6368 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tauhidi ginshikin Musulunci (1)

DSP Imam Ahmad Adam Kutubi

Yau cikin yardar Allah za mu fara tsakuro wani abu ne daga littafin Kitabut Tauhid da DSP Imam Ahmad Adam Kutubi ya fassara kuma ya aiko mana muna fata za a karu da abin da littafin yake karantarwa; Bismillah:

Babi na daya

Dalilin halittar mutum da aljan:

Allah Ya ce a cikin Alkur'ani Mai girma, "Ban halicci mutum da aljan ba, sai don su bauta Min. Ba Na bukatar wani arziki daga gare su, kuma ba Na neman su ciyar da Ni. Lallai ne Allah, Shi ne Mai azurtawa kuma Ma'abucin karfi." (Zariyati, 56-58). A wata aya kuma Allah Yana cewa, "Hakika kowace al'umma Mun aika mata da wani Manzo a kan su bauta wa Allah su nisanci dagutu." (Nahli, 36). Ma'anar dagutu, duk wani abin da ake bautawa ba Allah ba, kamar Mala'iku ko Annabawa ko aljanu ko waliyai ko salihai da sauransu.

A wata aya kuma Allah Yana cewa, "Hakika Allah Ya yi horo a kan a bauta maSa Shi kadai, kuma a kyautata wa iyaye biyu. Koda dayansu ya tsufa ko dukansu biyu, idan magana ta tashi tsakaninka da su, kada ka ce musu tir, kada kuma ka yi musu tsawa. Ka yi musu magana kyakkyawa ka tausasa musu, kuma ka nuna kai ba komai ba ne a gabansu. Idan kuma za ka yi musu addu'a, sai ka ce, ‘Allah Ka jikan mahaifana kamar yadda suka raine ni tun ina karami har na girma." (Isra'i, 23). Kuma a wata ayar, sai Allah Ya ce, "Ku bauta wa Allah Shi kadai, kada ku hada Shi da kowa." (Nisa'i, 36).


(Labarin Cikakkun... | 6368 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

Sabuwar Shekarar 1409 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi
(Labarin Cikakkun... | 8405 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Sabuwar Shekarar 1409 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi

Godiya da yabo da tsarkakewa sun tabbata ga Allah wanda Ya sanya dare da wuni su kasance ma'aunan gane lokuta. Kuma Ya sanya su domin gane kwanaki da shekaru da kuma lissafi.

Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa wanda aiko shi ya zama salsalar fitar da mutane daga duffan zalunci da shirka da tabewa zuwa ga hasken adalci da imani da shiriya.

A yau Juma'a ce muka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1409 Bayan Hijirar Annabi (SAW), kuma muna fata Allah Ya yi mana dandazon alheri a cikinta. Kuma Ya raba mu da sharri da bala'in da duk wata cutarwa da suke cikinta.

Bayan haka, hakika mafi yawan Musulmin Najeriya, suna gafala daga al'amarin sabuwar shekarar Musulunci, sun fi sanin watanni da kidayar shekarar Nasara wadanda ka gina su kan kalandar Gregory. Wannan ya sa da yawan Musulmi ba su ma sanin yaushe shekarar Musulunci ke shigowa ba, wani ma ba ya sanin kwanan watan Musulunci nawa ne sai lokacin azumi ko Sallah. Musulmi da dama a yau da za a tsare su a ce su lissafa watannin Musulunci sai dai su shiga kame­kame, ba su san su ba, kuma ba su nufin su sani!


(Labarin Cikakkun... | 8405 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Abin da za mu yi Allah Ya so mu (2)
(Labarin Cikakkun... | 6990 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Abin da za mu yi Allah Ya so mu (2)

Mu sake tambayar kanmu, "Shin Allah Yana sonmu?" Idan har muna ji a jikinmu cewa Allah ba Ya son mu saboda ba mu aikata abin da ya dace, to 'yan uwa mu yi wa kanmu kiyamul laili, mu tuna da karashen wannan Hadisi da muka fara kawowa, mu guje wa abin da zai fusata Allah. Mu guji mutanen da suke aikata ayyukan da suke fusata Allah.

Domin Manzon Allah (SAW) ya fadi a karshen Hadisin cewa: "Idan kuma Allah Ya ki mutum (saboda saba maSa), zai kira Mala'ika Jibril (AS) Ya ce masa: "Ya Jibrilu! BawaNa wane dan wane yana ci gaba da fusata Ni, don haka fushiNa ya tabbata a gare shi."

Ke nan samun so daga Allah yana ta'allaka ne da bin abin da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi na daga ayyukan da'a.

Kuma Allah Yana daukar duk wanda ya yi maSa biyayya a matsayin masoyinSa. Shi ya sa za mu ga Alkur'ani da Sunnah cike suke da darussan da suke nuni kan yadda za mu samu soyayya daga Allah Subhanahu Wa Ta'ala.

Babban ginshikin samun soyayya a tsakanin bawa da Ubangijinsa, shi ne yin imani da yin aiki nagari. "Lallai wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai (nagari), wadannan su ne mafifita alherin halitta. Sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shi ne gidajen Aljanna koramu na gudana a karkashinsu, suna madauwama a cikinsu har abada. Allah Ya yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa." (k:98:8).


(Labarin Cikakkun... | 6990 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Abin da za mu yiAllah Ya so mu (1)
(Labarin Cikakkun... | 6830 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Abin da za mu yiAllah Ya so mu (1)

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulki Ranar Sakamako. Kai kadai muke bautawa kuma gare Ka kadai muke neman taimako. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da sauran masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Bayan haka ganin halin da mu Musulmi muka samu kanmu a ciki a wannan lokaci, ya kamata mu rika wa kanmu wannan tambaya ta sama. "Shin Allah Yana sonmu kuwa?"

Yin Tambayar zai sa mu yi kokarin gano amsa kuma ta haka ne za mu iya gane ko muna tafiya a kan hanyar da Allah Yake so ko a'a. Na fadi haka ne saboda yadda muka iske kanmu a cikin wani yanayi na rana kuna inuwa zafi a kusan duk duniyar Musulmi.

Domin amsa wannan tambaya za mu leka tarihi mu ga yadda magabatan kwarai (Salafus Salih) da mamayan kwarai (Khalfus Salih) suka gudanar da rayuwarsu har suka samu daukakar da yanzu muke ta karantawa a littattafan tarihi da na addini, kuma suka zama su ne suke juya duniya a zamaninsu.

Bayan wafatin Annabi (SAW) ba da dogon lokaci ba, Abu Idris Alkhaulani (wanda ya rasu a shekara ta 80 Bayan Hijira daidai da shekara ta 699-700 Miladiyya) a Damaskus ta kasar Syriya ya tafi Masallacin Al-Kabir. A cikin masallacin ya iske rukunin mutane sun kewaye wani mutum. Ya bayyana siffar mutumin da mutum mai yawan murmushi kuma mutanen sun kewaye shi suna yi masa tambayoyi. Sai Abu Idris Al-Khaulani ya tambaya: "Wane ne wannan mutum?" Sai suka amsa: "Mu'azu bin Jabal ne (RA), sahabin Manzon Allah (SAW)."


(Labarin Cikakkun... | 6830 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Falalar Darare Goma na Zul-Hajji
(Labarin Cikakkun... | 7732 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Falalar Darare Goma na Zul-Hajji

Allah Madaukaki Ya ce: "Ina rantsuwa da Alfijir. Da Darare Goma." (Alfajr:1-2). Malamai sun kai sun kawo kan wadanne ne Darare Goma. Kuma mafi rinjaye sun tafi a kan darare goma na farkon watan Zul Hajji ne, kamar yadda Ibnu Kasir ya ce: "Darare Goma: Ana nufin goman Zul Hajji ne kamar yadda Ibnu Abbas da Ibnu Zubair da Mujahid da malamai da dama na Salafus Salih da Khalafus Salih suka fadi." (Tafsirul ku'anil Azim, mujalladi na 4 shafi na 539-540).

Ibnu Sa'adi (Rahimahllah) ya ce, "A bisa mafi ingancin magana su ne dararen goma na Ramadan ko darare goma na Zul Hajji. Su darare ne da suka kunshi ranaku masu falala, ayyukan ibada da neman kusanci ga Allah suna aukuwa a cikinsu fiye da wasunsu… A cikin darare goma na Zul Hajji ne ake tsayuwar Arfa wanda Allah Yake yin gafara ga bayinSa, gafarar da Shaidan ke bakin ciki da ita, domin Shaidan bai taba ganin kaskanci da tozarci irin na Ranar Arfa ba, saboda abin da yake gani na sassaukar Mala'iku da rahama daga Allah a kan bayinSa, kuma ayyukan Hajji da Umara na gudana a cikinsu. Wadannan abubuwa masu girma sun cancanci Allah Ya yi rantsuwa da su." (Taisirul Karimir Rahman, mujalladi na 7 shafi na 621-622).

An karbo daga Ibnu Abbas (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: "Babu ranakun da ayyuka nagari suka fi soyuwa a wurin Allah daga wadannan ranaku goma (na Zul-Hajji). (Sahabbai) Suk ce, Ya Rasulullahi! Ko da jihadi a tafarkin Allah? Ya ce, "Ko da jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai daga cikinsu ba." (Buhari). Ibnu Rajab ya ce: "Wannan Hadisi ya nuna aiki a cikin ranakunsa (Ranaku 10 na Zul-Hajji) ya fi soyuwa a wurin Allah daga aiki a sauran ranakun duniya ba tare da toge komai daga gare su ba. Kuma idan ya kasance mafi soyuwa ga Allah, to shi ne mafi falala a wurinSa." (Lada'iful Ma'arif, shafi na 458).


(Labarin Cikakkun... | 7732 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji
(Labarin Cikakkun... | 10430 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji

Babban Limamin Masallacin Nagazi-Ubete, Okene, Jihar Kogi

Mukaddima:

Bayan haka ya bayin Allah! Daga cikin muhimman lokuta na yin ibada akwai ranaku 10 na farkon watan Zul-Hajji – wata na 12 na shekarar Musulunci, wadanda Allah Ya fifita a kan sauran kwanaki na shekara.

Ibn Abbas ya ruwaito cewa: "Annabi (SAW) ya ce: "Babu wani aiki da ya fi alheri irin wanda aka yi a ranaku 10 na farkon Zul-Hajji." Sai wadansu sahabbai suka ce: "Koda jihadi a tafarkin Allah?" Annabi (SAW) ya ce: "Koda jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya tafi da kansa da dukiyarsa bai dawo da komai ba." (Buhari).

Wadannan kwanaki goma manya ne kuma mafiya soyuwa ne a wurin Allah. Ibn Umar (RA) ya ruwaito cewa: "Annabi (SAW) ya ce: "Babu wasu ranaku da suka da girma kuma suka fi soyuwa a wurin Allah fiye da wadannan kwanaki goma na farko Zul-Hajji, don haka ku yawaita tahlili da takbiri da tahmidi a cikinsu" (Musnad Imam Ahmad). Kuma Sheikh Ahmad Shakir ya inganta shi.

Daga cikin darajojin da wadannan kwanaki goma suke da su akwai cewa:


(Labarin Cikakkun... | 10430 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)
(Labarin Cikakkun... | 5942 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)

Tambaya: Mene ne hukuncin wuce Mikati ba tare da Harama ba,?

Amsa: Hakan ya halatta, matukar cewa ba ka zo ne da niyyar yanka ba, ya halatta ka shiga Makka ba tare da Harama ba, idan ka zo ne ba da niyyar Umara ko Hajji ba, kawai dai ka zo ne don wani dalili naka kamar neman ilimi ko duba mara lafiya, ko kasuwanci, kai ko ma a ce hanya ce ta biyo da kai, wannan babu komai a kanka. Wanda dole sai ya shiga da Harama shi ne wanda ya zo don aikin Hajji ko Umara, idan ya wuce ba tare da ya yi Harama ba, to sai ya zubar da jini, ma'ana sai ya yi yanka.

Tambaya: Ni mutumin kasar Sa'udiyya ne ina aiki a wajen kasar, a watan azumi na zo, iyalaina suna Jiddah, na fara sauka a wajensu na yi kwana uku, daga baya na yi Haramar yin Umara, shin ina da laifi?

Amsa: Wannan zuwa ka zo ne don iyalanka, sai bayan ka je gida sannan ka yi niyyar yin Umara, yin haka babu laifi, sai ka yi Harama a Jiddah kamar yadda mutanen Jiddah za su yi.

Tambaya: Ni ma'aikaci ne ina aiki a Riyad, sai na zo Jiddah don yin fasfo, bayan na gama abin da nake sai na yi niyyar yin Umara, na yi Harama daga Jiddah, bayan kwana uku na sake yin wata Haramar don yi wa mahaifiyata Umara, na yi Harama daga Mikatin Nana A'isha, sai kuma na yi niyyar yi wa mahaifina da ma wadansu mutane daban Umara, tare da cewa mahaifina da mahaifiyata sun rasu, shin abin da na yi niyya ya halatta?


(Labarin Cikakkun... | 5942 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)
(Labarin Cikakkun... | 6565 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)

Tambaya: Mene ne hukuncin mutumin Makka wanda yake so ya yi Umara, zai yi harama daga gidansa ne ko sai ya je Tan'im ko Ja'aran zai daura harami?

Amsa: Bai halatta ya yi harama daga gida ba, idan ya yi haka sai ya yi yanka (fidiya), sai dai ya yi harama daga Hillu, domin ko a ina bangaren gidansa yake abin da ake so shi ne ya fita wajen gari ya yiwo harama daga can.

Tambaya: Mu mutanen Makka ne, mun saba kowane watan Ramadan muna yin Umara amma daga gidajenmu muke daukar Harama, sai kuma mu tafi Tan'im mu dauki niyya, shin hakan da muka yi ya yi ko dole sai a Tan'im za mu daura Harami ?

Amsa: Abin da kuka yi ya yi babu laifi, matukar cewa ba ku yi niyyar Umara ba sai a Hallu, to hakan ya halatta, insha Allah babu laifi.

Tambaya: Matata ta zo daga Gabas da dadewa ba ta yi Umara ba, sai yanzu take so ta yi, shin sai na mayar da ita inda Mikatinsu yake ta yi Harama, ko ta yi Haramarta a Makka tunda a nan muke a zaune ?


(Labarin Cikakkun... | 6565 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Giba da illolinta (1)
(Labarin Cikakkun... | 7612 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Giba da illolinta (1)

Masallacin Harami na Ka'aba, Makka

Fassarar Salihu Makera

Huduba ta farko

Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman gafararSa muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma Ya batar babu mai shiryar da shi. Mun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya, kuma mun shaida Shugabanmu Annabi Muahmmad bawanSa ne kuma ManzonSa. Allah Ya kara tsira da amince a gare shi da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa.

Bayan haka, ina yi mana wasiyya da bin Allah da takawa, wanda ya yi maSa takawa Ya isar masa, wanda ya ji tsoron mutane ba su isar masa. Ina yi mana wasiyya da takawa, wadda ba Ya karbar waninta, kuma ba Ya jinkan kowa sai ma'abutanta, ba Ya bayar da lada sai a kanta, masu wa'aztuwa da ita suna da yawa, amma masu aiki da ita kalilan ne, Allah Ya sanya mu cikin masu takawa.

Ya ku Musulmi! Addinin Allah ya cika ya kammala, ya kunshi akida da shari'a da tauhidi da ibada da mu'amala da dabi'u, yana zance da hankali da zuciya da jiki da rai a cikin al'amuran da suka shafi shari'a da halaye da tarbiyya, addini daga Ubangijinmu yana tsara dokoki da rayuwa ga Musulmi mai mutunci da tsarki na zahiri da badini. Ya zamo Musulmi mai kubutacciyar zuciya, mai kame harshe, mai da'a ga Ubangijinsa mai halin kirki ga jama'a. Mai kokarin tsare mutuncinsa da kin bin son rai. "Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lallai sashen zato zunubi ne. Kuma kada ku yi rahoto, (bincikar laifin mutane)." (K: 49:12).


(Labarin Cikakkun... | 7612 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)
(Labarin Cikakkun... | 4755 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)

Tambaya: Shin wajibi ne ga mai iko duk shekara sai ya yi aikin Hajji, ko kuwa sau daya ne yake wajibi?

Amsa: Ba dole ba ne sai an yi duk shekara, na wajibi sau daya ne a rayuwa. Koda kuwa mutum yana da iko, ba ya zama dole a kansa, kamar yadda ya zo a cikin Hadisai da dama cewa Manzon Allah (SAW) ya tara mutane ya yi musu Huduba ya kwadaitar da su kan aikin Hajji. Sai wani Sahabi mai suna Akara'u dan Habis ya mike ya ce: "Ya Ma'aikin Allah shin duk shekara sai an yi? Sai ya ce: "A'a, da na ce eh da sai ya zama wajibi, sau daya ake aikin Hajji).

Tambaya: Wanda ya zo don yin Umara shin dole ne sai ya yi Hajjin wannan shekara? Saboda muna jin mutane suna fadar hakan shin gaske ne?

Amsa: Wannan kuskure ne, babu wanda ya fadi hakan cikin Malaman Musluunci.

Tambaya: Shin ya Halatta ga yaran da ba su kai shekara bakwai ba su yi dawafi tare da mahaifansu?

Amsa: Ya Halatta su yi haramar Hajji ko ta Umara, ko da ba su kai shekaru bakwai ba, kamar yadda ya zo a kissar matar nan Khas'imiyah wacce ta dauko karamin yaro da ke cikin shimfidar goyo (shawul) ta ce: ya Ma'iakin Allah (SAW)! Shin wannan zai iya yin Hajji? Ya ce: "kwarai kuwa amma ladan naki ne." Ta nan aka gane cewa Umarar yaron da bai kai shekaru bakwai ba ta halatta, kuma yana iya yin Hajji da dawafi amma a matsayin nafila.


(Labarin Cikakkun... | 4755 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Yadda Musulunci ya 'yanta mace (5)
(Labarin Cikakkun... | 2849 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Yadda Musulunci ya 'yanta mace (5)

Mutumin da ba ya da kishi shi ake kira da Larabci da Duyus, wato mai tabbatar da kazanta a cikin iyalinsa, wato mutum ya zamo gaso-rogo ko mijin Hajiya, babu ruwansa da masu shiga kan iyalinsa ko masu hulda da su. Malamai sun ce: "Duyus shi ne wanda ba ya kishin iyalin gidansa, kuma an samu gargadi mai tsanani tare da yi masa tattalin azaba a kan haka. An karbo daga Abdullahi dan Umar (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Mutum uku Allah Madaukaki ba zai dube su (da idon rahama) ba a Ranar Alkiyama: Mai guje (saba) wa iyayensa da mace mai shigar maza da kuma Duyus (namiji marar kishin matarsa)" (Ahmad da Nisa'i suka ruwaito).

Nuna kishi ga hurumin kamewa rukuni ne sananne da ke kare martaba da dabi'un mutane a zamanin Jahiliyya da kuma bayan zuwan Musulunci. Domin shi, wata dabi'a ce da dan Adam ya ginu a kanta, dabi'a ce mai kyau da tsabta. Duk mutumin da ba ya da kishin iyalinsa, ba ya da bambanci da dabba. Domin dabba ce kawai ba ta kishin muharraminta.


(Labarin Cikakkun... | 2849 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Yadda Musulunci ya 'yanta mace (4)
(Labarin Cikakkun... | 7698 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Yadda Musulunci ya 'yanta mace (4)

4 – 10. Runtse ido da tsare farji da sauransu:

Manufar shari'ar Musulunci ita ce kare martabar mace wadda ita ce ginshikin iyali. Kuma kare martabarta zai tabbata ne kawai idan aka hana abin da zai kai ga yaduwar zinace-zinace. Zinace-zinace kuwa masominsu shi ne gwamutsuwar maza da mata da bayyana kawa da kallo a karshe kuma a auka wa keta martabar mace. Musulunci ya umarci maza da mata su runtse daga ganinsu kuma su tsare farjojinsu daga aikata zina. (k:24:30-31)

Musulunci ya hana mata bayyana ado ko kawarsu face ga mazansu da wadansu da shari'a ta ambata. (k:24:31). duk wadda ta yi tawaye ga wannan doka sai mu ajiye ta a sahun mushirikai da kafiran Yamma.

Musulunci ya hana mata sassautar da magana ga mazan da ba na su ba don kada su ba masu muguwar zuciyar damar su yi tsammanin wani abu daga gare su. "Ya matan Annabi! Ba ku zama kamar kowa daga (sauran) mata ba in kuka yi takawa, saboda haka kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cuta a zuciyarsa ya yi tsammani…" (k:33:32). Musulunci ya haramta kebanta da ajaniba ko yin tafiya ga mace ba tare da muharraminta ba. An karbo daga Ibn Abbas (RA) ya ce: "Na ji Annabi (SAW) yana huduba yana cewa: "Kada namiji ya kebanta da mace face tare da ita akwai muharraminta, kuma kada mace ta yi tafiya sai tare da muharrami." Sai wani mutum ya tashi ya ce: "Ya Manzon Allah! Lallai matata ta tafi aikin Hajji, ni kuma an rubuta ni cikin masu tafiya yaki kaza da kaza." Sai (SAW) ya ce: "Tashi ka tafi aikin Hajji tare da matarka." (Buhari da Muslim). Ibn Hajrin ya ce, "A cikinsa (Hadisin) akwai hanin kebanta da ba'ajanabiya kuma shi ne ijma'in malamai." (Fathul Bari: 4/92). Alkali Iyal ya ce, "Mace fitina ce kuma an hana kadaita da ita ce, saboda abin da aka halicci zukatan maza na sha'awa a kansu (mata), kuma aka sallada Shaidan a tsakaninsu…." (Ikmalul Mu'allim: 4/448). Haka Musulunci ya hana shiga gidan da mace take ba tare da muharraminta ba. Ukbatu bin Amir (RA) ya ruwaito cewa: "Manzon Allah ya ce: "Kashedinku da shiga gidajen mata!" Sai wani mutum daga Ansar ya ce: "Ya Manzon Allah koda matan dan uwa ne (wa ko kane)?" Sai (SAW) ya ce: "Matan dan uwa mutuwa ce!" Khurdabi ya ce: "Fadinsa matar dan uwa mutuwa ce" na nufin shigarsa gidan matar dan uwansa yana kama da mutuwa wajen ki da barna. Wato abin haramtawa ne. An kai iyaka ne wajen gargadi aka kwatanta da mutuwa…. (Almufham:4/501).


(Labarin Cikakkun... | 7698 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Illolin zina da luwadi da madigo (1)
(Labarin Cikakkun... | 6911 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Illolin zina da luwadi da madigo (1)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin Manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam) tare da alayensa da sahabbansa. Bayan haka, wannan tsokaci ne a kan ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncin kowanensu a karkashin shari'ar Musulunci da Dokta Muhammad Rabi'u Umar Rijiyar Lemo ya rubuto kuma muka ga ya dace a sanya a wannan fili don amfanin jama'a. Ina rokon Allah Ya sa abin ya yi tasiri a kan kowane Musulmi. Bismillah!

Ma'anar zina da hukuncinta:

Lafazin zina a shari'ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure, ko an mallake ta a matsayin baiwa ba. Sai dai akan yi amfani da lafazin zina a kan abin da bai kai saduwa ba, kamar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ) ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "An rubuta wa dan Adam rabonsa na zina, babu makawa sai ya same shi, zinar idanu ita ce gani, zinar kunnuwa ita ce ji, zinar harshe ita ce magana, zinar hannu ita ce damka, zinar kafa ita ce taku, zuciya kuwa tana kwadayi tana fata, farji kuma shi yake gaskata haka ko ya karyata." Muslim.


(Labarin Cikakkun... | 6911 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Wani abu kan Sallar Idi
(Labarin Cikakkun... | 5943 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Wani abu kan Sallar Idi

A yayin da ranar Litinin mai zuwa ta kasance ranar Babbar Sallar bana, sakamakon cewa za a hau Arfa a jibi Lahadi, mun gabato da wata fadakarwa kan abubuwan da suka kamata mu yi da wadanda za mu guje musu a wannan rana ta farin ciki kamar haka:

Sallar Idi da ladubbanta:

Malamai sun hadu cewa ta kowane hali ko dalili a ranakun Idi biyu a hana yin azumi, koda na bakance ko kaffara ne kamar yadda Imam Annawawi ya nakalto a sharhinsa ga Sahihu Muslim. (8/15). Kuma sun ce, hikimar hanin ita ce idan aka yi azumin kamar an ki amincewa da liyafar da Allah Ya shirya ga bayinSa ne. (Nilul Audar, 4/262).

Sannan Sunnah ce, a yi wanka a sanya sababbin kaya ko a wanke wadanda suka fi kyau a sanya, kuma a fesa turare a fita masallacin Idi, maza da mata manya da yara tare da tsare ladubban fitar, wato kada mata sun caba ado ko su sanya turare kuma kada a cakuda maza da mata da sauran abubuwan da shari'a ta hana.

Ranar Sallah ranar ce ta murna da farin ciki da bukukuwa, to, sai dai kada wajen murna a wuce gona da iri. Kada murna ta sanya a koma ga sabo. Kada murna ta sa a aikata bidi'o'in da za su bata kyawawan ayyuka.


(Labarin Cikakkun... | 5943 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

Layya da hukunce-hukuncenta
(Labarin Cikakkun... | 7374 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Layya da hukunce-hukuncenta

Abin da ake cewa Layya shi ne duk wani abu da aka yanka domin neman kusanci ga Allah. Layya na da asali a cikin Alkur'ani da Hadisin Annabi (SAW). Allah (TWT) Yana cewa: "Ka yi Sallah ga Ubangijinka kuma ka yi yanka." (Kausar: 2) A Hadisi kuwa Anas Bin Malik (RA) ya ruwaito cewa: "Manzon Allah (SAW) ya yi Layya da raguna biyu bakake, masu kahonni. Ya yanka su da hannunsa, ya yi bisimillah ya yi kabbara, ya kwantar da su ta gefensu." (Muslim).

A shekara ta biyu Bayan Hijira aka shar'anta yin Layya kuma sunnah ce mai karfi a kan:

1. Musulmi da, namiji ko mace. Tana zama sunnah a kan mutum ga kansa da iyayensa, idan talakawa ne, da 'ya'yansa maza da ba su balaga ba ko mata da ba su yi aure ba. Ba sunnah ba ce mutum ya yanka wa matarsa ko dansa da aka haifa a ranar Layyar.

2. Kada ya kasance mahajjaci, domin shi mahajjaci, hadaya ce a kansa.

3. Ya zama ba matalauci ne ba, da ke cikin tsananin bukata. Amma zai iya cin bashi ya yi Layyar, idan ya san zai iya biya, ba tare da takura ba. Wasu malamai sun ce kada mutum ya ci ba shi domin yin Layya.

Dabbobin da ake yin Layya su ne: Rago wanda ya shekara, taure sai ya shiga shekara ta biyu. Sa, wanda ya shekara uku, rakumi sai ya kai shekara biyar. A wajen Layya, rago ya fi falala, sai taure, sai sa, sai rakumi. A cikin dukkan dabbobin an fi fifita maza a kan matansu da lafiyayyunsu (wadanda suke yin barbara) a kan fidiyayyuns, sai idan fidiyayyun sun fi kitse sai a yi da su.


(Labarin Cikakkun... | 7374 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
(Labarin Cikakkun... | 6889 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)

Na Khalid Bin Salamah

Fassarar Imam DSP Ahmad Adam Kutubi

Manufa ta Biyu: Tabbatar da girman Allah Madukaki:

Allah Ta'ala Ya ce: "Wancan ke nan. Kuma wanda ya girmama ibadojin Allah, to lallai ne (ita girmamawar) tana daga ayyukan zukata na ibada." (AI-Hajji). Su kuwa kalmomin sha'a'ir da mash'ar; su ne duk wani abu da ya sanya jin girman Allah da wadatuwarSa a cikin zuciya, da kaskancin abin halitta da bukatuwarsa, wannan kuwa yana bayyana karara a kasar Muzdalifa. To tsarkin ya tabbata ga Wanda wuyaye suka risina ga girmanSa. Hakika duk wanda ya kwatanta tsakanin yanayin alhazai a Mina da Arfa ta wani bangaren da kuma- yanayinsu a Muzdalifa a daya gefen, zai lura da bambancin mai zurfi a tsakanjn yanaye-yanayen guda biyu, wadanda su ne cewa alhazai a kasar Mina da Arfa bambancin matsayinsu yana bayyana karara ta bangaren wadata da talauci, cikin irin hemominsu da abincinsu da abin hawansu.

A dai Mina da Arfa za ka samu talakan da yakan zauna da yunwa a gefen hanya, kuma za ka samu mawadacin da yakan ja hankali da hemarsa da yanayin tufarsa da kuma kayansa.

Kai ta kai wani lokacin ma alhazai na iya shagaltuwa a nan da yanayin shiga ta ababen halitta ga barin wadatar Mahalicci Mai tsarki, kuma su shagala da girman ababen haiitta ga barin girman Mahalicci wanda tsarki ya tabbata gare Shi, har ma wadansu gafalallun zukata kan kusa su manta wane ne Mai girman ma a lokacin!


(Labarin Cikakkun... | 6889 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
(Labarin Cikakkun... | 8626 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)

Na Khalid Bin Salamah
Fassarar Imam DSP Ahmad Adam Kutubi

ambaya: Saboda me duga-dugan Manzo (SAW) masu alfarma ba su taba kasar Arafa ba a Hajjin Ban-Kwana?

Yana daga abin da aka sani yanke cewa Manzon Allah (SAW) abin so ne a wajen kowane mumini, haka nan gurabansa (abubuwan da ya bari kamar tufafi da abubuwan da ya yi amfani da su) su ma ababen so ne, kuma ma da yawa mutane na nemansu, kuma hakika Allah Ya yi nufin kada wani gurbin wani abin so ya kasance a Arafa ban da Shi Maddaukakin Sarki, koda kuwa guraben Manzon Allah (SAW) ne. Watakila hikamar haka- Allah Shi ne Mafi sani – ita ce da a ce Manzon Allah (SAW) yana da wani gurbi a Arafa da wadansu mutane sun rataya da ita su shagala da ita ga barin soyayyar Allah Ta'ala a wannan wuni mai girma, kuma da zukata sun karkata zuwa ga soyayyar bawa ga barin soyayyar Ubangiji Mai tsarki. Yaya haka kuwa ba zai auku ba, alhali mu mun sani cewa mafi yawan dalilin da mutane suka bata ta hanyarsa
shi ne wuce gona da iri cikin soyayyar salihan bayi da gurabensu.

Ashe shirka ta farko a bayan kasa a zamanin Annabi Nuhu (AS) ba ta kasance ta dalilin zurfafawa ba ne-cikin soyayyar salihai da gurabensu? Shin Nasara (Kiristoci) ba sun bata ba ne da shisshigi cikin soyayyar Annabi Isa (AS)? Hakan Rafidawa ba sun bata ba ne ta hanyar wuce gona da iri cikin soyayyar Aliyu da Husain (Allah Ya yarda da su)? Kuma wadansu daga cikin Sufaye sun bata ne saboda zurfafawarsu cikin soyayyar Jilani da waninsa. Sun so su irin son da ya yi kafada-da-kafada da sonsu ga Allah Mabuwayi, Madaukaki, sai suka halaka a cikin haka.


(Labarin Cikakkun... | 8626 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

Matsayin sada zumunta a Musulunci
(Labarin Cikakkun... | 6854 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Matsayin sada zumunta a Musulunci

Ma'anar sada zumunci:

Sada zumunta shi ne kyautatawa da jinkai da bibiyar 'yan uwa (ma'abuta zumunta), ta hanyar sadar da dukkan alheri gare su da kawar da dukkan sharri daga gare su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu'ar alheri, duk bangare ne na sada zumunta.

Har ila yau, ma'anar zumunta na game yin sallama ga dan uwa yayin haduwa da gaishe shi da ce masa yarhamukallahu idan ya yi atishawa ya ce alhamdulillahi.

Sannan zuwa duba dan uwa yayin da yake rashin lafiya da jajanta masa kan wata asara da ya yi da taya shi farin cikin samun wani alheri da rufa masa asiri da rike amanarsa da kare mutunci da martabarsa a kan idonsa ko a bayansa a boye ko a bayyane da yi masa nasiha da shawara ta alheri duk sada zumunta ne.


(Labarin Cikakkun... | 6854 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

Sallar Idi da ladubbanta
(Labarin Cikakkun... | 4956 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Sallar Idi da ladubbanta

Malamai sun hadu cewa ta kowane hali a ranakun Idi biyu a hana yin azumi, koda na bakance ko kaffara kamar yadda Annawawi ya nakalto a sharhinsa ga Sahihu Muslim. (8/15). Kuma sun ce, hikimar hanin ita ce idan aka yi azumin kamar an ki amincewa da liyafar da Allah Ya shirya ga bayinSa ne. (Nilul Audar, 4/262).

Sannan Sunnah ce, a yi wanka a sanya sababbin kaya ko a wanke wanda suka fi kyau cikin tufafin mutum, a sa turare a fita masallacin Idi, maza da mata manya da yara tare da tsare ladubban fitar, wato kada mata sun caba ado ko sun sanya turare kuma kada a cakuda maza da mata da sauran abubuwan da shari'a ta hana.

Ranar Sallah ranar ce ta murna da farin ciki da bukukuwa, to, sai dai kada wajen murna a wuce gona da iri. Kada murna ta sanya a koma ga sabo. Kada murna ta sa a aikata bidi'o'in da za su bata kyawawan ayyuka.

Daga cikin ladubban murnar Sallah akwai:

1. Taya juna murna da duk lafazin da ya sauwaka, kamar "Allah Ya karba mana da makamancin haka. An ruwaito cewa wasu daga magabatan kwarai sun aikata haka. Misali Jubairu bin Nufair ya ce, "Sahabban Annabi (SAW) idan suka hadu da juna sukan ce, "Allah Ya karba mana, Ya karba muku." Imam Ahmad ya ce Isnadinsa mai kyau ne, sannan Hafiz ya kyautata Isnadinsa a cikin Fathul Bari (2/517), kuma a duba Tamamul Minnah na Albani don karin bayani. Kuma an ruwaito Imam Ahmad yana cewa: "Ba zan fara fada wa mutum haka ba, amma idan ya fada min zan amsa." Shi kuma Shaihul Islam Ibnu Taimiyya (RH) ya ce, "Fara taya murna ba Sunnah ce da aka yi umrni da ita ba, kuma ba a hana ba, wanda ya aikata, ya yi koyi, wanda ya ki, ya yi koyi." Majmu'u Al Fatawa (24/253). Hakika irin wannan gaisuwa na yin tasiri wajen karfafa zumunta da ruhin soyayya a tsakanin Musulmi.


(Labarin Cikakkun... | 4956 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Tukuici ga mai azumi (4)
(Labarin Cikakkun... | 7157 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tukuici ga mai azumi (4)

Nafilfilin dararen goma na karshen watan Ramadan:

Daga A'isha (Allah Ya yarda da ita),ta ce: "Annabi (SAW), ya kasance idan goman karshe na watan Ramadan ya zo, to ba ya barci, sai ya tada mutanen gidansa maza da mata ya dukufa da nafilfili har karshen watan Ramadan." Buhari ya ruwaito.

I'itikafi:

Shi I'itikafi shi ne mutum ya zauna a masallaci don nafilfili da karatun AIkur'ani da zikiri da addu'o'i don neman dacewa daga Allah a duniya da Lahira. Shi kuma Sunnah ne da ake so, amma abin da aka fi so daga goman karshe na watan Ramadan. Kuma an ce karancinsa kwana daya da wuni, amma akasarinsa kwana uku. Awata ruwaya kuma an ce karancinsa kwana uku, amma mafi yawansa kwana goma har zuwa wata guda. Kowanne ka zaba daga cikin wadannan maganganu ya yi daidai. An karbo daga A'isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Annabi (SAW) ya kasance yana I'ittikafi a kwana goma na karshen Ramadan har ya bar duniya.


(Labarin Cikakkun... | 7157 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Al'Adun Musulmi Da Darajoji

Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)
(Labarin Cikakkun... | 4338 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)

Shi kuma Salam bin Abu Mudi'u ya ce: "kattada yana sauke Alkur'ani a (kwana ko dare) bakwai, amma idan Ramadan ya zo a kowane uku. Idan goman karshe suka zo, sai ya rika saukewa a kowane dare." (Siyar A'alamin Nubla'i, 5/276).

Rabi'u bin Sulaiman ya ce: "Imam Shafi'i ya kasance yana sauke Alkur'ani sau sittin a cikin watan Ramadan." (Siyar A'alamin Nubla'i, 10/36). Akwai misalan haka da dama.

Tsayuwar Ramadan:

An karbo daga Abu Huraira (RA) cewa: "Lallai Manzon (SAW) ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar Ramadan (Sallar Tarawihi ko Asham) yana mai imani kuma domin Allah kawai, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa." Buhari da Muslim suka ruwaito.

Aliyu bin Al-Madani ya ce: "Suwaidu bin Ghafalata ya rika yi mana limanci a tsayuwar Ramadan har ya kai shekara 120 a duniya." (Siyar A'alamin Nubla'i, 4/72).


(Labarin Cikakkun... | 4338 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

Tukuici ga mai azumi (3)
(Labarin Cikakkun... | 2464 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)

Tukuici ga mai azumi (3)

Wadanda azumi bai wajaba a kansu ba, amma dole su biya:

1. Matafiyi idan ya sha azumi a cikin tafiya dole ne ya biya.

2. Mara lafiya yana iya shan azumi duk lokacin da ya warke sai ya biya abin da ya sha.

3. Mai haila ba azumi a kanta, amma in ta yi tsarki za ta biya abin da ta sha, kuma idan mai haila ta dauki azumi sai jini ya zo mata kafin rana ta fadi, to, azuminta ya baci, haka nan kuma idan haila ya dauke mata da rana a Ramadan ba azumi a kanta a sauran wannan yinin sai dai za ta rama azumin ranar da sauran kwanakin da ta sha. Bugu da kari idan jinin ya dauke kafin fitowar alfijir ko da mintuna kadan ne kafin fitowar alfijir, to, azumi ya wajaba a kanta.
karin bayani: Shi ma jinin haihuwa (biki) kamar jinin haila ne cikin dukkan hukunce-hukuncensa.

4. Mace mai shayarwa idan ta ji tsoron danta ba zai samu nonon da za ta shayar da shi ba, sai ta ci abinci, to, tana iya cin abincin bayan azumi ya wuce sai ta rama gwargwadon abin da ta sha. Haka hukuncin yake ga mace mai ciki idan ta ji tsoron abin da ke cikinta, ita ma tana iya shan azumi kuma wajibi ne a kanta ta biya gwargwadon azumin da ta sha bayan ta haife cikin nata.


(Labarin Cikakkun... | 2464 Bytes Ƙari | Son yin sharhi? | Makinku Kan Labari: 0)
 


 

EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com